Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

Sanata Binani ta yi addu’a da fatan Allah kada ya sake saukar da irin wannan Iftila’i.

Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

Sanata Aisha Dahiru Binani ta bayar da tallafin Naira miliyan 50 domin taimaka wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri da Jere a Jihar Borno.

Ta bayar da tallafin ne yayin ziyarar da ta kai wa Gwamna Babagana Umara Zulum a Maiduguri a ranar Talata.

Binani, ta bayyana Maiduguri a matsayin gidanta, inda ta ce abin da ya ƙara mata karkashi, shi ne dangantakar da ke tsakaninta da garin da kuma buƙatar nuna goyon baya ga jama’ar jihar.

“Muna addu’a kada wani ya sake fuskantar irin wannan iftila’in a ko ina suke. Mun san mutanen Borno suna da ƙarfin zuciya da juriya. Muna rokon Allah Ya taimake su, su fita daga wannan masifa.

“Muna kuma addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu, Allah Ya sa suna aljanna, ya kuma bai wa iyalansu hakurin jure rashinsu,” in ji ta.

Tawagar ta haɗa da Ambasada Fatima Balla Abubakar, Sanata Ahmed Hassan Barata, da sauransu.

A martaninsa, Gwamna Zulum, ya gode wa Sanata Binani bisa ƙoƙarin da ta yi na ziyarar duk da rashin kyawun yanayi da hanya.

“Jiya jirgin Sanata Binani bai samu sauka ba saboda rashin kyawun yanayi, don haka suka koma Abuja. Na ce mata kada ta damu, amma ta nace cewar Borno gida ne a wajenta, kuma tana so ta nuna goyon bayanta da kanta. Wannan yana nuna ƙarfin zumunci tsakaninta da mutanen Borno,” in ji shi.

Ya nuna godiya bisa tallafin da ta bayar tare da tabbacin cewa za a yi amfani da kuɗin yadda ya dace.

“Kin bayar da Naira miliyan 50, kuma ina tabbatar miki cewa gwamnatin Borno za ta yi amfani da kuɗin yadda ya dace.

“Mun riga mun kafa kwamiti, wanda ya haɗa da mambobin ICPC da EFCC, don tabbatar da cewa kuɗin ya isa ga waɗanda suka cancanta.”

Gwamna Zulum, ya kuma bayyana Sanata Binani a matsayin ‘yar uwa ba abokiyar siyasa ba, tare da sake nuna godiyarsa kan kyautar da yi musu.