Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

Shugaban kamfanin na BUA ya kuma bayar da tallafin kayan abinci ga waɗanda ambaliyar ta shafa.

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

Mai Kamfani BUA, Abdulsamad Isyaka Rabi’u, ya bayar da tallafin Naira biliyan biyu domin taimaka wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri da Jere a Jihar Borno.

Babban Daraktan Kamfanin, Kabiru Rabi’u ne, ya wakilci Abdulsamad a yayin gabatar da tallafin ga Gwamnan Jihar Babagana Umaru Zulum a Maiduguri.

Kabiru, ya bayyana cewa, BUA ya bayar da tallafin kuɗi Naira biliyan ɗaya, sai kuma tallafin abinci na sauran Naira biliyan ɗaya.

Bugu da ƙari, BUA ya bayar da kyautar ƙarin tirela biyar ɗauke da buhun shinkafa 900, da ƙarin tirela biyar ta fulawa da kuma tirela biyar ɗauke da katon ɗin taliya 4500.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7