Ambaliya: dan majalisa ya kai dauki a Damagun
dan Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai wakiltar mazabar Damagum a karamar Hukumar Fune Alhaji Abdu Mamman Zoto ya kai tallafin kayan abinci ga al’ummar mazabarsa da suka hadu da ambaliyar ruwan sama a garin Ngelzarma.Da yake bayani ga Aminiya a garin Damaturu dangane da tallafin, dan majalisar ya ce ambaliyar ruwan da ta auka wa […]
dan Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai wakiltar mazabar Damagum a karamar Hukumar Fune Alhaji Abdu Mamman Zoto ya kai tallafin kayan abinci ga al’ummar mazabarsa da suka hadu da ambaliyar ruwan sama a garin Ngelzarma.
Da yake bayani ga Aminiya a garin Damaturu dangane da tallafin, dan majalisar ya ce ambaliyar ruwan da ta auka wa al’ummar Ngelzarma lamari ne daga Allah Wanda Ya kaddara faruwarsa.
dan majalisar ya ce akwai bukatar gwamnatin jiha ta kara sa hannu wajen tallafa wa jama’ar domin lamarin ya yi matukar ta’azzara saboda magidanta da yawa sun rasa muhallinsu da
abin da za su ci.
Ya yaba kokarin gwamnatin jihar na tallafa wa jama’ar da ambaliyar ta shafa, sai da ya ce dukn da haka akwai bukatar ta sake yin wani abu a kai.
Kayayyakin tallafin da dan majalisar ya kai wa al’ummar Ngelzarma sun hada da buhunan hatsi 100 da katon din taliya100 da Maggi katun 10, sai man girki jarka 20 da buhunan gishiri 10 da tattasai da borkono da kuma tumatiri buhuna shida.
Ya roki Gwamnatin Tarayya ta taimaka wa al’ummar Ngelzarma saboda abubuwa sun yi yawa ga gwamnatin jihar.