Ambaliya: Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri — NCS
Hukumar ta ce tana aiki tuƙuru don sake cafke fursunonin da suka tsere.
Hukumar da ke Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCS), ta ce fursunoni 281 ne, suka tsere sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafe wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Kakakin hukumar, Umar Abubakar, ya ce: “Wannan lamari mara daɗi ya haifar da ɓarna, inda ya rushe katangarar gidajen gyaran hali da suka haɗa da matsakaicin cibiyar tsaron hukumar ta Maiduguri (MSCC).”
- Yiwuwar ɓarkewar cuta: An gargaɗi ’yan Maiduguri kan sayen kayan lambu
- An Kama Shi Kan Kisan Dan Shekara 28 A Damaturu
Ya bayyana cewa: “Bayan kwashe fursunonin da jami’an hukumar tare da tallafi daga jami’an tsaro zuwa wani waje mai tsaro, sai aka gano fursunoni 281 sun ɓace.”
Ya ƙara da cewa hukumar tana da bayanan fursunonin da suka tsere
Ya ce: “Hukumar tana aiki tare da sauran jami’an tsaro saboda an fara aikin a ɓoye domin ƙara kama su.
“A yanzu haka, an sake kama fursunoni bakwai tare da mayar da su gidan yari, yayin da ake ƙoƙarin gano sauran don a dawo da su.
“Yayin da ake wannan ƙoƙarin, akwai tabbacin cewa lamarin ba zai kawo cikas ba ko kuma ya shafi lafiyar jama’a ba.”