Ambaliya: Gini ya yi ajalin uba da ɗa a Jigawa
Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki sama da 1,000 a yankin cikin kwanaki uku.
Wani magidanci da ɗansa mai shekara biyu, sun rasa rayukansu bayan da gini ya rushe tare da danne su a garin Madabe, da ke ƙaramar hukumar Buji a Jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi, bayan tafka mamakon ruwan sama a yankin.
- Gwamnatin Kano ta janye dokar hana fita gaba ɗaya
- Ambaliyar ruwa ta shafe hanyar Jigawa zuwa Bauchi da Gombe
Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Buji, Alhaji Ali Safiyanu, ya tabbatar da faruwa lamarin a ranar Litinin.
Ya ce matar mutumin mai shekara 25 ce kaɗai, ta tsira bayan samun raunuka, inda tuni aka kai asibiti domin kula da ita.
Kakakin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a jihar, Badaruddeen Tijjani, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai bayyana sunan waɗanda lamarin ya shafa ba.
Tuni hukumomi suka fara bincike kan musabbabin rushewar ginin.
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 400 tare da lalata gonaki kusan 1,000 daga ranar Alhamis zuwa Lahadi.