Ambaliya: Gwamnatin Gombe ta bai wa Maiduguri tallafin N100m
Ambaliyar ita ce mafi muni cikin shekaru 30 da suka gabata.
Gwamnatin Jihar Gombe ta jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno bisa mummunar ambaliyar ruwa da ta afka wa garin Maiduguri, babban birnin jihar.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda mataimakinsa, Manassah Daniel Jatau, ya jagoranci wata tawaga a madadinsa, ya mika tallafin Naira miliyan 100 a matsayin taimako ga wadanda lamarin ya shafa.
- Yadda Hausawa ke gudun sunayensu na asali zuwa na gargajiyar Larabawa
- Matatar Dangote za ta fara rarraba man fetur ranar Lahadi
A yayin ziyarar da tawagar ta kai gidan gwamnati da fadar Shehun Borno da ke Maiduguri, mataimakin gwamnan ya isar da ta’aziyyar gwamna da al’ummar Jihar Gombe.
Ya bayyana cewa ziyarar ta zama wajibi ne, saboda kyakkyawar alakar da ke tsakanin jihohin biyu.
Cikin wata sanarwa da daraktan watsa labaran gwamnatin, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana cewa gwamnan, wanda ya fita ziyarar aiki a ƙetare, ya umurci a gaggauta kai ziyara ga Jihar Borno saboda dangantaka ta musamman da ke tsakanin jihohin.
A martaninsa, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya nuna matukar godiya kan yadda Gwamnatin Gombe ta nuna damuwa da kauna a wannan lokaci.
Ya kuma gode wa gwamnatin Gombe kan tallafin Naira miliyan 100 da ta bayar.
Ya yi alkawarin amfani da kudin cikin adalci domin rage radadin ambaliyar.
Bugu da ƙari, tawagar ta kai ziyara Fadar Shehun Borno, Mai Martaba Alhaji Garbai Al’amin Elkanami.
Mataimakin gwamnan, Manasseh Daniel Jatau, ya jajanta wa mutanen Borno kan rasa rayuka da dukiyoyi, tare da yin addu’ar Allah Ya ji ƙan wadanda suka rasa rayukansu a sanadin ambaliyar.
A nasa jawabin, Shehun Borno ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa aiko tawagar domin yi musu jaje.
Ya bayyana cewa wannan ambaliyar ita ce mafi muni idan an kwatanta da wadda ta faru shekaru 30 da suka gabata.
Tawagar Gombe ta kuma kai ziyara wasu yankunan da ambaliyar ta shafa a garin Maiduguri domin duba barnar da aka yi.