Ambaliya: Gwamnatin Jigawa ta ware N835m don ba da agaji
Gwamnatin ta ce ta fara ɗaukar matakan ne domin kaucewa asarar rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamnatin Jihar Jigawa, ta ware sama da Naira miliyan 835 domin sayen kayan agajin gaggawa, a wani yunƙuri na fuskantar ambaliyar ruwa da ka iya faruwa a shekarar 2026.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Dutse.
- Matashi ya kashe maƙwabcinsa kan jarkar ruwa a Sakkwato
- ’Yan bindiga sun kai hari makaranta, sun kashe malami tare da sace ɗalibai a Kogi
Ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen sayen kayan abinci, kayan sawa da kuma kayan gini domin taimaka wa mutanen da ambaliya ko wani iftila’i ka iya shafa.
A cewarsa, Majalisar Zartarwa ta jihar ta bai wa Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) izinin sayen kayayyakin tare da adana su a wurare daban-daban domin a samu damar kai agaji cikin sauri idan buƙatar hakan ta taso.
Ya bayyana cewa kayan abinci za su taimaka wa iyalan da suka rasa matsugunansu, yayin da kayan sawa da na gini za su tallafa wa waɗanda gidajensu ko dukiyoyinsu suka lalace sakamakon ambaliya.
Kwamishinan, ya ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman a lokacin damina.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da ambaliya ke yawan aukuwa da su bi shawarwarin hukumomi tare da bai wa jami’an agaji haɗin kai domin sauƙaƙa ayyukan ceto da kai ɗauki.
A cewarsa, gwamnatin Jigawa na ɗaukar matakan kariya tun kafin aukuwar ambaliya domin rage asarar rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.