Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta bai wa Borno tallafin 100m
Zulum ya jinjina wa jihar kan yadda ta ke taimakon mutanen Borno.
Gwamnatin Jihar Yobe, ta bai wa Gwamnatin Jihar Borno tallafin Naira miliyan 100 domin taimakon waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne, ya miƙa tallafin a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga Gwamna Babagana Umara Zulum a Maiduguri.
Buni, ya kuma sanar da bayar da tallafin kayan abinci na Naira miliyan 50 ga waɗanda Iftila’in ya shafa.
“Jihohin Yobe da Borno tamkar tagwaye ne da suka fuskanci irin wannan halin kuma suna buƙatar goyon bayan juna,” in ji shi.
Buni, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu a ambaliyar da kuma samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Gwamna Zulum, ya yaba wa gwamnatin Yobe game da taimakon da suke bai wa jihar.
“Mutanen jihohin Yobe da Borno sun kasance iyali ɗaya ne, abin da ya shafi ɗaya, ya shafi ɗaya.
“Ina alfahari da cewa mai girma yayana Gwamna Mai Mala Buni tun hawansa mulki a matsayin gwamnan Jihar Yobe, ya ƙara danƙon zumunci da ’yan uwantaka tsakanin jihohin Borno da Yobe fiye da kowane lokaci.
“A lokuta da dama gwamnatinku ta kan bayyana tare da nuna irin dangata ta iyali daya da mutanen Jihar Borno.
Zulum, ya ce “Gwamnati da jama’ar Borno suna matuƙar godiya ga mai girma gwamna bisa wannan karamci.”