Ambaliya: Kamfanin Media Trust ya bai wa Maiduguri tallafin N10m
Rukunin Kamfanin Media Trust, mamallakin Jaridar Daily Trust, da Aminiya, da Tashar Talabijin ta Trust TV, da kuma tashar rediyo ta Trust Radio tare da haɗin gwiwa da Gidauniyar Daily Trust ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 ga mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri, Jihar Borno. Ɗaya daga cikin daraktocin kamfanin, Malam Mannir […]
Rukunin Kamfanin Media Trust, mamallakin Jaridar Daily Trust, da Aminiya, da Tashar Talabijin ta Trust TV, da kuma tashar rediyo ta Trust Radio tare da haɗin gwiwa da Gidauniyar Daily Trust ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 ga mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri, Jihar Borno.
Ɗaya daga cikin daraktocin kamfanin, Malam Mannir Ɗan Ali ne ya sanar da haka a lokacin da suka kai ziyarar jaje wurin Gwamna Babagana Umaru Zulum a ranar Asabar.
A yayin wannan ziyara, Mannir Ɗan Ali ya samu rakiyar Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin, Malam Ahmed Shekarau tare da Shugaban Ofishin Kamfanin da ke Maiduguri, Hamisu Kabir Matazu.
A jawabinsa na godiya, Gwamna Zulum ya jinjina wa Media Trust yana mai nanata cewa ba wannan ne karon farko da kamfanin yake tashi tsaye ba wajen bayar da tallafi musamman a lokutan da ake da tsananin buƙata.