Ambaliya: Kashi 80 na dabbobi sun salwanta a gidan adana namun dawa a Maiduguri
Ambaliyar ta yi awon gaba da wasu muggan dabbobi masu cutarwa da suka haɗa da kada da macizai
Fiye da kashi 80 cikin 100 na dabbobin da ake tsare da su a gidan adana namun daji da ke Maiduguri na Jihar Borno sun tsere sakamakon ambaliyar ruwan da ta mamaye sassa da dama a birnin.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar hukumar kula da gidan adana kayan tarihi da namun dawa ta Jihar Borno ta fitar.
- ASUU ta ayyana yajin aiki a Jami’ar Gombe
- Tinubu ya kunyata waɗanda suka kyautata masa zato — Sarkin Yaƙin Yarbawa
Babban manajan hukumar, Ali Abatcha, shi ne ya bayyana hakan da cewar ambaliyar ruwa ta lalata kadarori da ta janyo asara mai girman gaske a gidan adana namun dawa.
Ya bayyana damuwa game da lamarin, yana mai cewa akwai fargaba kan lafiyar jama’a bayan tserewar dabbobin.
Dabbobin da ke gidan zoo na Sanda Kyarimi, ciki har da zakuna da kadoji da karkanda da dai sauran halittu sun mutu, yayin da wasu da dama ruwa ya yi awon gaba da su.
Babban Manajan ya yi gargaɗin cewa ambaliyar ta yi awon gaba da wasu muggan dabbobi masu cutarwa da suka haɗa da kada da macizai zuwa yankunan da ke kusa.
Don haka ya gargaɗi jama’a da su yi taka tsan-tsan don gujewa waɗannan dabbobi masu haɗari da ake fargabar sun shiga cikin al’umma.
Ya ba da tabbacin cewa ana ɗaukar matakan tabbatar da tsaro da kare sauran dabbobi da ma’aikatan da ke cikin gidan namun dajin.
Daga ƙarshe ya yi addu’ar Allah Ya kawo mana sauƙin wannan iftila’in tare da yin kira ga ‘yan ƙasa da su koma ga Allah Ta’ala domin samun sauƙi.
Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Farar Hular a yankin Tafkin Chadi, Ahmed Shehu ya ce, kawo yanzu babu wanda ke da masaniya kan halin da dabbobin ke ciki bayan sun tsere daga gidan adana namun daji na Shehu Sanda Kyarimi.
“Lamarin na da ban-tsoro, ambaliyar ruwan ta mamaye gidan adana namun dajin. Kodayake babu wanda ya san halin da dabbobin ke ciki, amma tabbas za su nemi mafaka, sai dai akwai yiwuwar su cutar da bil Adama.”
Aminiya ta ruwaito cewa, an dai samu mummunar ambaliyar ruwa sakamakon katsewar Madatsar Ruwan Alau da ke birnin Maiduguri, wanda hakan ya jefa dubban al’ummar yankin cikin mawuyancin hali na rasa muhalli da kuma fargabar ɓarkewar cututtuka har ma da asarar rayuka.