Ambaliya: Kungiyar Likitoci na fargabar barkewar annoba a Najeriya

An bukaci gwamnati ta yi kokarin samar da tsaftataccen ruwan sha a kauyukan da ambaliyar ta shafa.

Ambaliya: Kungiyar Likitoci na fargabar barkewar annoba a Najeriya

Kwamitin Kula da Aukuwar Bala’o’i da Fadakarwa kan annoba na Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), ya shawarci gwamnatocin Najeriya a dukkan matakai, da su daura damarar dakile barkewar annoba dalilin ambaliyar ruwa da aka samu a kasar.

Shugaban Kwamitin, Dokta Abubakar Hassan ne ya sanar da hakan a Lokoja, babban birnin Kogi a ranar Litinin

Kwamitin ya roki gwamnatocin da su yi kokarin samar da tsaftataccen ruwan sha ga kauyukan da ambaliyar ta shafa, kasancewar hanyoyin samar da ruwan yankunan sun gurbace.

Sanarwar ta kuma yaba da kokarin Gwamnatin Tarayya na samar da na’urar tace ruwan sha a kasar, tare da kiran a sanya yankunan da aka samu ambaliyar cikin wadanda za a samawa na’urar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta kara kulawa da kauyukan da abin ya shafa, tare da rabon gidajen sauro, domin dakile cizon kwari, musamman Sauro da Kudajen Tsandu da ke sanya cutar bacci.

An ceto wani yaro da aka sace, an kama mutum 4 Gombe

Fursunoni 52 sun zana jarabawar kammala sakandare a Kano

Mutum 18 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Neja

Amurka ta janye sojojinta daga Najeriya