Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA
Ambaliyar ta shafi aƙalla mutum 119,791 a bana — kuma mafi akasari mata ne da yara.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) ta ce aƙalla mutane 165 ne suka rasu, sannan 82 suka ɓace sakamakon ambaliya a bana.
NEMA ta bayyana haka ne a ranar Juma’a a wata ƙididdiga da ta fitar, tana mai cewa ambaliyar ta shafi aƙalla mutum 119,791 a bana — kuma mafi akasari mata ne da yara.
- Dadiyata: Buhari ya gaza nemo shi, Tinubu yana da lokaci — Amnesty
- Mutum ɗaya ya rasu, an jikkata wasu yayin arangama da ’yan sanda a Abuja
Ta bayyana cewa mutane 138 sun samu raunuka iri-iri, 43,936 sun rasa matsugunansu, gidaje 8,594 da gonaki 8,278 ne ambaliya ta shafa a cikin ƙananan hukumomi 43 da ke jihohi 19.
Ta ce, “Yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304 da kuma mutane 1,863 masu nakasa ne ambaliya ta shafa a bana.”
Jihohin da suka fi yawan waɗanda ambaliya ta shafa sun haɗa da Imo, Ribas, Abia, Borno da Kaduna.
A halin yanzu, jihohi 19 da ambaliya ta shafa sun haɗa da: Abia, Abuja, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Ribas da Sakkwato.