Ambaliya na iya ɓarna a fiye da rabin Nijeriya — Gwamnati

NNPCL ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar nan kan ambaliyar ruwa.

Ambaliya na iya ɓarna a fiye da rabin Nijeriya — Gwamnati

Wata ambaliyar ruwa a Jihar Kogi

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa daga wannan wata na Yuli jihohi 19 da Birnin Tarayya, Abuja za su fara fuskantar ambaliyar ruwa da ake hasashen za ta yi barna sosai.

Gwamnatin ta kuma yi gargaɗin cewa ambaliyar za ta jawo ta’azzarar cutar kwalara a wasu jihohin.

Aminiya ta ruwaito a makon jiya cewa aƙalla mutum 2,000 ne suka kamu da cutar kwalara, inda sama da 63 suka rasu.

Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utseb, ya ce ambaliyar da ake gani tun daga watan Mayu, somin-tabi ne, kuma ya ce toshe hanyoyin ruwa ke haddasa ta.

Ya ce daga watan Yulin manyan kogunan kasar nan za su fara tumbatsa suna ambaliya, wanda hakan zai sa matsalar ta ta’azzara.

Jihohin da za su yi fama da matsalar su ne: Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Binuwai, Kuros Riba, Delta, Edo, Jigawa, Kaduna, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Ribas, Taraba sai Birnin Tarayya, Abuja.

Ministan ya ce ana hasashen samun ambaliya daga Kogin Kwara da Kogin Binuwai, inda ya kara da cewa mutanen jihohin su fara shirin kauce wa hanyoyin ruwan.

Ya ce suna shirye-shiryen gina ƙananan dam-dam don tarewa da adana ruwan da ke ambaliya daga Dam ɗin Lagdo na kasar Kamaru, wanda ambaliyarsa ke barna sosai a Nijeriya.

Ministan ya ce har kwamitin Shugaban Kasa aka kafa don tabbatar kare aukuwar ambaliyar a bana.

Shi ma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Yanayi, Mista Clement Nze, ya ce hukumarsa ta yi hasashen cewa kananan hukumomi 148 a jihohi 31 za su fuskanci matsalar ambaliya a bana.

Sai dai ya ce Gwamnatin Tarayya ta dauki matakan da suka kamata, sannan ta mika wasu tsare-tsare da kayayyakin aiki da gwamnatocin jihohi domin daukar matakan da suka dace.

Aminiya ta lura cewa kusan duk shekara akan yi fama da ambliyar, duk da a farkon damina hukumomi kan fitar da gargadin yiwuwar aukuwar ambaliyar, amma ba a cika daukar matakan da suka dace don hana aukuwarta ba.

Matsalar da a lokuta da dama, sai ta auku, a rika kai agajin gaggawa, sannan a ci gaba da rayuwa har wata shekarar ambaliyar ta sake iskar mutane.

A Jihar Yobe, inda a bara aka fuskanci ambaliya mai muni, mutane na ganin ba a dauki matakan da za su hana aukuwarta ba a bana, inda suke tsoron matsalar za ta fi kamari a bana.

Yobe tana da manyan koguna kamar Kogin Komadugu da Kogin Hadeja da ya hadu da kogin na Yobe wanda ya karade kusan dukkan kananan hukumomin Arewacin jihar da a duk shekara al’ummomin da ke gabar kogin ke fuskantar ambaliyar da ke yi musu barnar gidaje da amfanin gona da lalatata hanyoyin mota.

A bara, ambaliyar ta tayar da kauyuka 11 a kananan hukumomin Gujba da Gulani inda magidanta sama da 100 suka rasa muhallinsu, kuma ta lalata hanyoyin mota, musamman hanyar Buni Gari zuwa garin Bara hedikwatar Karamar Hukumar Gulani.

Malam Abdullahi Hussaini wani mazaunin Karamar Hukumar Jakusko ya bayyana wa Aminiya cewa yadda suka fara ganin daminar bana ta sauka sun fara fargabar abin da zai kasance saboda tuno shekarar 2022 da shekarar 2023 inda suka fuskanci ambaliyar da ta kai ga lalata hanyoyin mota a yankin da janyo sauran matsaloli.

Gwamnatin Mai Mala Buni ta yi kokari a wancan lokaci wajen ganin al’ummomin da ambaliyar ta yi awon gaba da gidajensu sun koma muhallansa dalilin daukin da Hukumar SEMA ta kai musu.

Haka a barar ambaliyar ta yi awon gaba da hanyoyin mota a Arewacin Yobe kamar hanyar da ta tashi daga garin Damaturu ta nufi kananan hukumomi Bursari, Geidam, Yunusari, Bade da kuma Jumhuriyyar Nijar, inda mazauna yankin suka ce suna fargabar za a iya maimaita abin da ya faru a bara, ko ma ta fi kamari a bana.

Sai dai a bangaren gwamnati, ta ce tuni ta fara daukar matakin gyara hanyar, inda ta ce zuwa yanzu an samu sauki.

Gwamnan Jihar ya bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta kafa wani kwamitin da zai kula da faruwar ambaliyar don samun saukin daukar matakin gaggawa.

A makon jiya Daraktan Hukumar SEMA ta Jihar Yobe Dokta Mohammed Goje da hadin gwiwar Hukumar Acresal sun shirya bitar kwana guda ga masu ruwa-da-tsaki a jihar dangane da yadda za a tunkari yiwuwar aukuwar ambaliya a jihar.

Da yake bayani a wajen taron Dokta Goje ya ce sun kira taron ne don fadakar da jama’a tare da sanar da su hanyoyin da ya kamata su bi domin kiyaye ambaliyar, tare da daukar matakin gaggawa idan ta auku.

Fadada magudanun ruwa ya magance matsalar ambaliya a Suleja

Garin Suleja da ke Jihar Neja ya fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a unguwanni da ke wajen garin a lokuta da dama, inda aka yi asarar rayuka masu yawa da salwantar dukiya.

Suleja ta samu gagarumin kwararar jama’a daga yankunan Birnin Tarayya, Abuja da matsalar rusa gine-gine ta shafa a shekarun baya, inda bakin ko masu ba su gidajen haya, suka gina gidaje ciki har da wurare da ke kusa da rafuka ko manyan magudanun ruwa.

Lamarin ya yi ta haifar da ambaliya ciki har da mafiya muni da suka auku a watannin Yulin shekarar 2017 da 2020, a tarihin yankin.

Daga cikin wadanda ambaliyar ta rutsa da su, akwai iyalan wani magidanci mai suna Sa’adu Abubakar Asha da ya rasa mace da ’ya’ya 7 a ambaliyar shekarar 2017, kuma ruwa ya shafe gidansa, ya koma tsakiyar rafin da ya ratsa unguwarsu a Unguwar Kaduna Road a Suleja. Ambaliyar ta 2017 ta shafi unguwannin da ke makwabtaka da suka hada da Bakin-Iku da Hayin-Nasara a Suleja.

Malam Sa’adu Asha wanda ya samu tallafin Gwamnatin Jihar Neja a lokacin don saye ko sake gina wani gida a wani wajen daban, ya rasu bayan kamar shekara uku da aukuwar ambaliyar da ta shafe iyalansa baki daya.

A mafi yawan lokuta, ambaliyar na faruwa ce da dare inda kusan kowa ke kwance a gida.

An sake samun wata ambaliyar a shekarar 2020 wadda aka bayyana a matsayin wadda muninta ya dara ta baya, inda kusan mutum 20 suka rasu a yankin na Suleja.

A wancan lokaci ambaliyar ta shafi unguwannin Rafin-Sanyi da Uguwar Gwari, sai yankunan Kwankwashe da Madalla, duka a karamar hukumar.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su shi ne Mista Igbomara Thank-God, wanda ya rasa matarsa mai juna biyu da ’ya’yansa hudu.

Ambaliyar da ita ma ta zo cikin dare, ta ci bangaren gidansa da ke gefen rafin da ya ratsa unguwarsu, Unguwar Gwari.

Haka nan bala’in ya shafi wasu karin unguwanni a yankin Rafin-Sanyi Suleja da suka hada da Polosa da Unity, sai unguwanni biyu a garin Madalla da ke yankin, inda ya ci rayuka da kuma rusa gidaje.

Wakilinmu da ya sake komawa yankin a ranar Litinin da ta gabata, ya samu labarin cewa matakin da Gwamnatin Jihar ta dauka bayan faruwar ambaliyar biyu, na rusa daukacin gine-gine da suka rage a gefen rafukan da ke yankunan, tare da tabbatar da cewa ba a bar wani ya sake mayar da gini a wuraren ba, wanda hakan ya taimaka wajen magancen aukuwar wata ambaliyar.

Haka kuma an gina gadoji masu tsawo da suka dara wadanda ambaliyar ta malale.

Gadojin bayan wadanda yawanci al’ummar unguwannin ke yin su, a lokuta da dama tarikice bola kan makale a jikinsu daga kasa, sannan ruwa ya shafe samansu dalilin gajertansu da kankantarsu.

A zantawa da wakilinmu a yayin ziyarar, Malam Isa Lawan, Mai Unguwar Unity ya bayyana jin dadinsa da gina manyan gadoji uku da gwamnatin jihar ta yi bayan ambaliya ta biyu a unguwannin Polosa da Unity sai kuma wadda aka yi a Unguwar Gwari.

Mai unguwar ya gode wa Allah kan tsayawar ambaliyar bayan wadda ta auku a shekarar 2020. Ya ce abin a yaba ne yadda gwamnatin ta yi tsayuwar daka wajen ganin ba a bar mutane sun sake yin gini a kan hanyan magudanun ruwa ba.

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Jigawa

Jihar Jigawa na cikin jihohin da ake hasashen ambaliyar za ta illata a bana, sannan tana cikin jihohin da suke fuskantar matsalar sosai.

A bara said a ambaliyar ta tayar da garuruwa da dama a jihar, sannan aka yi asarar gonaki da dama.

A bana ma, tuni ambaliya ta fara afka wa kauyen Kargo da ke Karamar Hukumar Garki a Jihar Jigawa, lamarin da ya haifar da barna tare tilasta mutane kaurace wa gidajensu.

Ambaliyar wadda ta afku a ranar Asabar da ta gabata da tsakar dare, ta shafi sama da gida100, inda ta lalata dukiya ta miliyoyin Naira.

Ruwa ya mamaye kauyen, lamarin da ya janyo ambaliya ta gurbata rijiyoyi tare da lalata gidaje.

Ambaliyar ta tilasta wa mazauna kauyen da dama neman mafaka a asibitoci da makarantun da ke kusa, yayin da wasu suka makale a gidajensu, suna jiran taimako.

Dagacin kauyen, Ali Mainasara, ya bayyana lamarin a matsayin mummunan hali, inda ya ce mazauna kauyen da dama sun yi asarar gidaje da dukiyoyinsu.

Ya ce zuwa lokacin ba su iya kididdige dukiyoyin da aka yi asara ba, inda gidaje da dama suka ruguje, magidanta da dama na kuka kan yadda za su yi.

Babban Sakataren Hhukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Dokta Haruna Mairiga, ya ziyarci kauyen don tantance barnar da aka samu, sannan ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta bayar da taimakon da ya dace ga wadanda lamarin ya shafa.

Ya umarci ayarinsa ya taimaka wajen gina jinga da magudanun ruwa na gaggawa don karkatar da ruwa a idan aka samu ambaliyar a nan gaba.

Dama Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa ta bayyana kananan hukumomi 18 za su fuskanci ambaliya a jihar. Kuma daga bisani ta wayar wa yankunan kai game da hasashen da ta yi.

Ambaliyar ce ta jawo karancin man fetur — NNPC

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar nan kan ambaliyar ruwa da rashin kyawun yanayi.

Kusan mako guda ke nan da fara samun dogayen layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar nan, wanda hakan ya sa wasu gidajen man ƙara kudin man da suke sayarwa kan kowace lita.

Wata sanarwa da NNPCL ya fitar ta ce “Hakan ya faru ne sakamakon matsalar jigilar sauke man daga manya zuwa ƙananan jiragen ruwa.

“Haka nan, saboda hadarin da ke tattare da fetur da kuma bin umarnin Hukumar Kula da Yanayi cewa kada a yi jigilar mai yayin da ake tsaka da ruwan sama da tsawa, ba zai yiwu a yi dauko mai ana tsaka da tsawa da walkiya da kwarara ruwa ba.

“Haka matsalar ta ƙaru saboda ambaliya ta mamaye wasu hanyoyin manyan motoci, abin da ya kawo tsaiko a jigilar man daga tashohin ruwa zuwa Abuja,” in ji NNPC.

Samun dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur ba sabon abu ba ne a Nijeriya, inda a watannin baya aka samu irin haka, har wasu gidajen mai suka rika sayar da mai a farashin da ya haura Naira 1000 kan kowace lita.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC