Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe
Hukumar ta ta ja kunnen mutane da su yi amfani da kayan yadda ya dace.
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji.
An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko.
- Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon
- Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango
Kayan da aka bayar sun haɗa da shinkafa, taliya, man girki, da kuma tufafi, kayan mata da shadda.
Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin gaggauta tallafa wa al’ummar da ambaliyar ta shafa.
Ya kuma roƙi jama’a da su yi amfani da kayan agajin yadda ya dace.
A nasa jawabin, babban daraktan NEDC, Mohammed Goni Alkali wanda Dokta Ali Ibrahim Abbas ya wakilta, ya gode wa gwamnatin Yobe bisa shirin.
Ya ce wannan tallafi wani ɓangare ne na manufar NEDC na taimaka wa al’ummar Arewa Maso Gabas wajen magance matsalolin yankin.
An sa ran wannan tallafin zai rage wa jama’a wahalhalun da ambaliyar ruwa ta jawo a jihar.