Ambaliya: NEMA ta nemi jama’a su share magudanun ruwa a Edo

Wasu ƙananan hukumomin za su fuskanci ambaliya kamar yadda Hukumar Hasashen Yanayi (NiMet) ta bayyana.

Ambaliya: NEMA ta nemi jama’a su share magudanun ruwa a Edo

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta buƙaci mazauna yankin da masu ruwa- da-tsaki kan muhalli da su kan gudanar aikin share magudanar ruwa domin shirya wa tunkarar ambaliyar a Jihar Edo.

Shugaban Ofishin Hukumar NEMA a Jihar, Ɗahiru Yusuf ne ya yi wannan kira a Benin lokacin wani shiri na wayar da kan jama’a kan yadda ake sarrafa shara da kuma tunkarar ambaliyar ruwa, da aka shirya da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Edo (SEMA).

Ya ce taron an yi shi ne don wayar da kan jama’a da masu ruwa-da-tsaki a ɓangaren muhalli a fadin jihar, musamman waɗanda suke fama da matsalar ambaliya da nufin daƙile ambaliya da kuma samun tsabtataccen muhalli.

Ya ce, “Wasu ƙananan hukumomin za su fuskanci ambaliya kamar yadda Hukumar Hasashen Yanayi (NiMet) ta bayyana.

“Muna wayar da kan jama’a kan yadda ake sarrafa shara da kuma shirye-shiryen tunkarar ambaliya domin rage illarta.”

Sai ya buƙaci wakilan al’ummomi na ƙananan hukumomi su isar da wannan saƙo zuwa ga al’ummominsu domin gudanar da ingantaccen shiri na tunkarar ambaliyar.

A ɓangaren Daraktar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Edo (SEMA), Madam Helen Obayuwna, ta ce, ambaliyar ruwa a kullum tana haifar da asarar rayuka da raba jama’a da gidajensu, baya ga lalata ababen more rayuwa da kuma dakatar da harkokin karatu a makarantu da sauransu.

A jawabin Shugaban Ofishin Kula da Muhalli da Sauyin Yanayi na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Edo, Mista Frank Inenemhoi, ya ce rashin isassun ma’aikata da kuɗaɗe ne manyan matsalolin da sashi nasa yake fama da su, kuma hakan na taimakawa wajen kasa shirya taron faɗakarwa a kan yadda ake sarrafa shara da kuma kare kai daga ambaliyar ruwa.

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur