Ambaliya ta ci yankunan manoma 82 a Naje
Ambaliyar ta mamaye makarantu da cibiyoyin lafiya 90 a cikin kwanaki biyu a Karama Hukumar Mokwa
Aƙalla yankunan manoma 82 ne ambaliya ta mamaye a Ƙaramar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja.
Ambaliyar ta kuma mamaye makarantu da asibitoci 90, baya ga gonaki da sauran kadarori masu yawan gaske.
Ibtila’in ya faru ne bayan mamakon ruwan sama da aka tafka daga ranar Litinin zuwa Talata a yankunan.
Aminiya ta gano cewa a gundumar Muregi kaɗai ambaliyar ta mamaye yankuna 51, ragowar 31 kuma suna gundumar Gbara.
- An Sako Seaman Abbas Bayan Shekaru 6 A Tsare
- Yara 50m ke gararamba a titunan Najeriya —Gwamnati
- Cutar kwalara ta kashe mutane tara a Yobe
- Matar Gwamnan Akwa Ibom ta rasu
Ambaliyar ta mamaye makarantu 47 da cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 43 a yankunan Muregi, Gbara da Ja’agi da ke ƙaramar hukumar ta Mokwa.
Daraktan Yada Labarai na hukumar jinƙai ta jihar, Habibu Abubakar Wushishi, ya shaida wa Aminiya cewa mazauna yankunan da abin ya shafa sun yi ƙaura zuwa wurare masu aminci.
Ya jajanta musu tare da kira a gare su da su tashi daga wuraren da hukumar NiMet mai kula da yanayi ta yi hasashen samun ambaliya.