Ambaliya ta ci mutum 10 a Jihar Gombe

Kimanin mutum 10 ne suka rasu, inda magidanta da dama suka rasa muhalansu a ranar Juma’ar da ta gabata sakamakon ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka share sa’oi biyu ana yi a Jihar Gombe.Ambaliyar ta yi sanadiyar cikewar manyan titunan garin Gombe da yashi inda hakan ya haifar […]

Ambaliya ta ci mutum 10 a Jihar Gombe
Ambaliya ta ci mutum 10 a Jihar Gombe

Kimanin mutum 10 ne suka rasu, inda magidanta da dama suka rasa muhalansu a ranar Juma’ar da ta gabata sakamakon ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka share sa’oi biyu ana yi a Jihar Gombe.
Ambaliyar ta yi sanadiyar cikewar manyan titunan garin Gombe da yashi inda hakan ya haifar da cinkoson ababen hawa, kuma bayanai sun nuna ambaliyar ta karya wata gada da ke tsakanin Gombe da Bauchi.
Kwamishinar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Gombe, Misis Rabi Daniel, ta zaga wasu sassan fadar jihar don gane wa idonta yadda lamarin ya kasance tare da jajanta wa jama’ar da al’amarin ya shafa.
Kwamishina Rabi Daniel ta ce abin da ke kawo ambaliyar ruwan da shi ne cushewar magudanun ruwa sakamakon yadda wasu jama’a ke mayar da su wuraren zubar da shara da kuma yadda wasu ke gine-gine a kan hanyoyin ruwa ba bisa ka’ida ba.
Misis Rabi Daniel, ta yi kira ga jama’ar Gombe su daina zuba shara a magudanun ruwa, su rika zuba sharars a wuraren da aka tanadar don guje wa sake aukuwar ambaliyar nan gaba.
Kwamishinar ta kuma yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya su ci gaba da wayar da kan al’ummarsu illa toshe magudanun ruwa ko yin gine-gine a kan layukan ruwa.
Kwamishinar ta yi kira ga wadanda lamarin ya shafa su rungumi al’amarin a matsayin kaddara ce daga Ubangiji.
Wasu daga cikin unguwannin da Kwamishinar ta zaga sun hada da Unguwar Checheniya da Barikin ’Yan sanda da Kasuwar Shanu da bundu Wailaru da Gandu da Herwagana da Unguwa Uku da kuma Bolari, inda ta yi ta’aziyya ga ’yan uwan wadanda suka rasu tare da jajanta wa wadanda suka rasa muhalli da dukiyoyinsu.
Kwamishinar ta samu rakiyar Babban Sakataren Ma’aikatar da daraktoci da sauran ma’aikata.