Ambaliya ta hallaka daliban ATBU 4 a Bauchi

A wannan mako ne ambaliyar ruwa a ta jawo rasuwar mutum biyar, ciki har da daliban Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi inda wadansu da dama suka samu raunuka sannan aka yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira. Ambaliyar ta fi barna ne a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda mutum hudu suka […]

Ambaliya ta hallaka daliban ATBU 4 a Bauchi

A wannan mako ne ambaliyar ruwa a ta jawo rasuwar mutum biyar, ciki har da daliban Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi inda wadansu da dama suka samu raunuka sannan aka yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Ambaliyar ta fi barna ne a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda mutum hudu suka rasu, bakwai kuma suka samu raunuka sakamakon karyewar da wata gadar da dalibai ke bi suna zuwa dakunan kwanansu ta yi.

Sauran wuraren da wannan bala’i ya faru sun hada da garin Dindima da Liman Katagum da Ramin Kasa da Kafin Kuka  a Azare da wasu sassa a yankunan kananan hukumomin Bauchi da Katagum,

Da yake bayyana yadda daliban Jami’ar ATBU hudu suka rasu, Shugaban Jami’ar Farfesa Muhammed Ahmed Abdulazeez ya ce daliban sun rasu ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka a daren Litinin wanda ya dauki tsawon awoyi ana yi.

Shugaban Jami’ar ya ce tsautsayin ya faru ne a harabar jami’ar da ke Gubi, kuma daliban da suka rasu uku maza ne da mace daya, “Kuma mun fahimci cewa abin ya faru ne lokacin da daliban ke kokarin komawa dakunan kwanansu daga wajen da suke karatu, sai gadar ta karye,” inji shi.

Farfesa Abdulazeez ya ce, “Majalisar Gudanarwar Jami’ar ta yi taro inda ta yanke shawarar rufe jami’ar saboda alhini da kuma gaisuwar ta’aziyya domin martaba rayukan dalibanmu da suka riga mu gidan gaskiya, amma za a dawo makarantar a ranar 19 ga Agusta. Za mu rufe makarantar gaba daya ce saboda ba zai yiwu wani bangare na jimami  wani bangare kuma na aiki ba.”

Da aka tambaye shi me ya sa jami’ar ba ta gyara gadar ba domin dalibai sun ce sun yi ta kokawa, sai Shugaban Jami’ar ya ce  jam’o’i na fama da karancin kudi kwarai da gaske, kuma wannan gada da ma an yi ta ce don daukar dalibai goma kawai, amma akwai ainihin babbar hanya da za su bi sai dai hanyar tana da nisa.

Sai dai a lokacin da abin ya faru, daliban jami’ar sun yi zanga-zanga inda suka zargi jami’ar da rashin tabuka komai waje gyara gadar.

Wani dalibi ya ce dakinsu daya da daya daga cikin wadanda suka rasu, kuma ruwan ya same su ne lokacin da suke dawowa daga dakin karatu za su koma dakin kwanansu.

Wani jami’i a jami’ar ya shaida wa manema labarai cewa gadar ya kamata ta dauki mutum 10 ne amma lokacin da ruwa ya fara sai dalibai tsakanin 20 zuwa 40 suka hau a lokaci guda, kuma hukumar makarantar ta sa lantarki mai amfani da hasken rana amma wadansu batagari sun sace kayayyakin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Kamal Datti Abubakar ya ce rundunar ta tura jami’anta don tabbatar da tsaro, sai dai ya ce tunda abin ya faru a cikin jami’a, hukumar jami’ar ce ya kamata su yi bayani.

Sarkin Dindima Malam Sale Ubandoma ya ce mutum daya ya rasu a garinsa kuma ruwan ya tafi da gidaje sama da 100 da kuma barnata gonaki da dama.

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir wanda, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Abubakar Y. Suleiman ya wakilta tare da ayarinsa sun ziyarci wuraren da ambaliyar ta shafa, sannan ya yi alkawarin taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa.

Gwamnan ya ce ya zo wajen da abin ya faru ne domin gane wa idonsa irin barnar da ruwan ya yi, sannan ya umarci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar ta taimaka wa mutanen da tallafin gaggawa sannan ya yi alkawarin gyara gadar da ta karye a Liman Katagum cikin gaggawa.