Ambaliya ta hallaka mutum bakwai a Karu

A ranar Litinin din makon jiya ce ambaliya ta hallaka akalla mutum bakwai a garin Karu da ke karamar Hukumar Karu na Jihar Nasarawa.dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karu/Keffi/Kokona Honorabul Jonathan Gaza Gbefwi, wand ya ziyarci inda lamarin ya auku ya tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin, ya ce “Tabbas na shaida aukuwar wannan ambaliya domin […]

Ambaliya ta hallaka mutum bakwai a Karu
Ambaliya ta hallaka mutum bakwai a Karu

A ranar Litinin din makon jiya ce ambaliya ta hallaka akalla mutum bakwai a garin Karu da ke karamar Hukumar Karu na Jihar Nasarawa.
dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karu/Keffi/Kokona Honorabul Jonathan Gaza Gbefwi, wand ya ziyarci inda lamarin ya auku ya tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin, ya ce “Tabbas na shaida aukuwar wannan ambaliya domin na ziyarci wajen da kaina kuma na gani gidajen da suka ruguje fiye da 50 inda aka rasa rayukan mutane fiye da bakwai, domin har yanzu ba a gano gawarwakin wadansu da ake tunanin ruwa ya ci  su. Da ma gwamnati ta fada wa jama’a cewa bana za a yi ambaliya, don haka ya kamata mutane su yi hattara musamman masu gidaje kusa da manyan rafuka, na yi matukar bakin ciki kann aukuwar lamarin, koda yake lamarin Ubangijine  ba a yi maSa gyara.”
Ya kara da cewa ya tuntubi Shugaban Hukumar NEMA ta kasa kuma ya ce nan ba da jimawa ba zai je inda lamarin ya auku domin ya ba su shawarwarin da suka dace. “Kuma za mu je wurin Ministan Muhalli domin a san yadda za a bullo wa lamarin zaizayar kasa wadda a da  ba mu da ita. Kuma ina kira ga gwamnatin ta taimaka ta kawo wa al’ummar da lamarin ya shafa daukin gaggawa,” inji shi.
Sai ya yi ta’aziyya tare da jajanta wa wadanda lamarin ya shafa.