Ambaliya ta jawo asarar dukiya ta miliyoyin Naira a Nasarawa

Al’ummar Tudun kauri a karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa sun sake yin asarar kayayyaki na miliyoyin Naira sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin a karshen jiya. Ruwan wanda aka yi kusan awa uku ana yi ya haifar da ambaliya a gidaje da shagunan jama’a musamman wadanda suke kan […]

Ambaliya ta jawo asarar dukiya ta miliyoyin Naira a Nasarawa

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar NasarawaAl’ummar Tudun kauri a karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa sun sake yin asarar kayayyaki na miliyoyin Naira sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin a karshen jiya. Ruwan wanda aka yi kusan awa uku ana yi ya haifar da ambaliya a gidaje da shagunan jama’a musamman wadanda suke kan hanyar Lafiya zuwa Makurdi da kuma Agyaragun Tofa.
An ga mazauna yankin suna kokarin kwashe ruwa daga gidajensu yayin da wasu suke kokarin tattara kayayyakinsu da suka rage don canja mazauni.
Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin don gane wa idonsa yadda lamarin ya auku ya tattauna da wasu daga cikin mazauna yankin, Malam Musa Inusa da Alhaji Umaru Yahaya. Malam Musa Inusa ya ce “Ambaliyar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata bayan barnar da ta yi, ta kusa halaka wasu yara hudu inda sai da muka fada ruwan muka ceto su. Don haka muna rokon gwamnati ta taimaka a kawo karshen lamarin.”
Shi kuma Alhaji Umaru Yahaya ya yi kira ga gwamnatii jihar ne ta samar musu da magudanun ruwa a yankin don kawo karshen lamarin. Ya kuma shawarci al’ummar Tudun kauri su daina watsa shara a magudanar ruwa domin a cewarsa yin haka ne babban abin da ke taimakawa wajen aukuwar ambaliya a yankin.
Ya ce dole ne al’ummar yankin su tallafa wa kokarin gwamnatin jihar ta hanyar yashe magudanar ruwansu don ba ruwa damar wucewa ba tare da matsala ba.
Aminiya ta gano ambaliyar ta rusa wani gidan sama da ke kusa da makarantar firamari ta Tudun kauri da wasu gine-gine a yankin.
Idan za a iya tunawa Lafiya da kewayensa sun fuskanci ambaliyar ruwa a bara, wanda hakan ya kai ga asarar rayuka da dama da kuma dukiya ta miliyoyin Naira. Kuma tun daga lokacin ne gwamnatin jihar ta dauki matakan samar da manyan hanyoyi da magudanun ruwa domin kawo karshen al’amarin.