Ambaliya ta kashe magidanci da iyalansa a Kebbi

Magidanci da matarsa da ’ya’yansu hudu ne gini ya fado a kansu sakamakon ambaliya

Ambaliya ta kashe magidanci da iyalansa a Kebbi

Mutum shida ’yan gida daya sun mutu bayan gini gidansu ya fada a kansu a sakamakon amabliyar ruwa a Jihar Kebbi.

Ginin ya fada a kan wani magidanci da matarsa da ’ya’yansu hudu ne bayan kwana ruwan sama mai karfi na kusan awa biyu da aka yi da tsakar daren Litinin.

Wani mazaunin garin Lauwali Yaldu ya ce da babban dan magidancin shi ne kadai ya tsira, kasancewa yaron yana makaranta a lokacin da abin ya faru.

Lauwali Yaldu ya ce Iftila’in wanda ya ruwa wasu gidaje a garin, ya faru ne a lokacinda ba za ka iya kai wa iyalan dauki ba, a garin Tungar Gyado da ke Kauyen Kwanawa a Kasar Yeldu, Karamar Hukumar Arewa ta Jihar.

Tuni dai aka yi jana’izar mamatan aka kai su makwancinsu kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Mutuwar iyalan da aka yi jana’izarsu a ranar Litinin  ta jefa garin cikin juyayi a Jihar da ke fama da matsanancinyar ambaliya tare da jawo dimbin asara.

A rahotannin Aminiya na baya ta ruwaita ambaliya ta lalata amfanin gona da aka kiyasata sun kai Naira biliyan biyar, baya ga gidaje da asarar rayuka.

Ko a ranar Lahadi rahotanni sun nuna ambaliyar ruwan sama ta yi barna sosai a garin Argungu da ke jihar.