Ambaliya ta kashe mutum uku a kudancin Rasha

Wannan na zuwa ne bayan wata makamanciyar ambaliya da ta afku a yankin a makon da ya gabata.

Ambaliya ta kashe mutum uku a kudancin Rasha

Ambaliya sakamakon ruwan sama da ya zuba kamar da bakin ƙwarya ta kashe wasu mutane uku a kudancin Rasha, yayin da aka kwashe kusan mutum 4,000 daga muhallansu, a cewar ma’aikatar agajin gaggawa ta ƙasar.

Mahukunta sun ce ruwan ya mamaye gidaje da hanyoyi a yankin Dagestan, inda lamarin ya haddasa rushewar wani ɓangare na wani gini mai hawa da yawa a babban birnin yankin, Makhachkala.

A cewar ma’aikatar, mutum biyu ciki har da yaro guda sun mutu bayan ruwa ya mamaye wata babbar hanya har ya kifar da motoci biyu, yayin da wani mutum ya mutu sakamakon zabtarewar ƙasa.

An kuma dakatar da aikin wasu matatun ruwa saboda katsewar wutar lantarki, lamarin da ya ƙara tsananta halin da jama’a ke ciki.

Jami’an agaji da dama na ci gaba da aikin ceto, yayin da ake hasashen ƙarin ruwan sama a yankin.

Wannan na zuwa ne bayan wata makamanciyar ambaliya da ta afku a yankin a makon da ya gabata, wadda ta haddasa katsewar wutar lantarki da kuma ayyana dokar ta-ɓaci.