Ambaliyar Borno ta kashe ’yan Boko Haram a Dajin Sambisa

Mayaƙan kungiyar da matansu da ’ya’yansu sama da mutum 100 ne ruwan ya kashe a Sansanin Dollarland

Ambaliyar Borno ta kashe ’yan Boko Haram a Dajin Sambisa

Ambaliyar Jihar Borno ta kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sama da mutum 100 a maɓoyarsu da ke Dajin Sambisa.

Aminiya ta samu rahoto cewa ambaliyar ta hallaka mayaƙan Boko Haram din ne a sansaninsu na Dollarland, a Dajin Sambisa.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar mana cewa mayaƙan kungiyar da matansu da ’ya’yansu sama da mutum 100 ne ruwan ya kashe.

Majiyar ta ce da misalin karfe biyu na dare ne ambaliyar ta mamaye maɓoyar Boko Haram ɗin, suna tsaka da barci.

“Wurin mai nutsewa ne. Ruwan ya yi ambaliya ne daga Kogin Yedzaram ya shanye Dollarland da sauran wuraren baki daya.

“Abin ya girgiza ’yan Boko Haram ɗin, mutanen da suka binne sun fi guda 100,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa ambaliyar ta kuma tashi mayaƙan Boko Haram daga yankin Gwoza.

Ambaliyar ta kuma lalata wani ɓangare na tsohon gidan yarin kungiyar, har sai da suka fitar da wasu tsararru.