Ambaliya ta lalata daruruwan gonakin shinkafa a Taraba

Ambaliyar ruwa ta lalata daruruwan gonakin shinkafa a kananan hukumomin Gassol da Bali da ke Jihar Taraba. Gonakin shinkafar wadanda suke a gefen Kogin Taraba dukkansu ruwa ya mamaye su tare da haifar wa manoma  hasarar miliyoyin Naira. Wakilin Aminiya ya ce wuraren da barnar ta fi muni sun hada da  yankin Bali da Tella […]

Ambaliya ta lalata daruruwan gonakin shinkafa a Taraba

Manoman shinkafa sun yi asara sakamakon ambaliya a gonakinsu

Ambaliyar ruwa ta lalata daruruwan gonakin shinkafa a kananan hukumomin Gassol da Bali da ke Jihar Taraba.

Gonakin shinkafar wadanda suke a gefen Kogin Taraba dukkansu ruwa ya mamaye su tare da haifar wa manoma  hasarar miliyoyin Naira.

Wakilin Aminiya ya ce wuraren da barnar ta fi muni sun hada da  yankin Bali da Tella da Sardirde; inda dubban manoman shinkafar suka yi hasarar shinkafa wadda ke gab da nuna.

Wani manomi mai suna, Malam Yakubu Yuguda, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa ya shuka buhunan shinkafa uku kuma ya kiyasta cewa zai samu sama da buhunan shinkafa 120, amma ambaliyar  ruwar ta lalata gonarsa baki daya.

Ya ce manoma sama da 50 da ke yankin Tella, su ma ambaliyar ta lalata gonakinsu.

Ya bayyana cewa wadansu da suka yanke shinkafarsu, ruwa ya yi awon gaba da shinkafar kafin su gyara ta.

Wakilin Aminiya ya fahimci cewa dubban manoman ne ke noma shinkafa a gabar Kogin Taraba mai tsawon kimanin kilomita 300 kuma ambaliyar ta mamaye daukacin gonakin da ke gabar kogin.

Wani manomi, Malam Bello Maigari, ya shaida wa wakilinmu cewa a yankinsu na Sardirde dubban manoman  shinkafa sun yi hasarar shinkafar wadda ke ganiyar nuna a sanadiyyar ambaliyar ruwan.

Ya kara  da cewa yankin na samar da shinkafa mai yawan gaske a duk shekara a jihar:  amma wannan matsalar ta ambaliya za ta haifar da karancin shinkafa a bana a jihar. Manomin ya ce, akasarin manoman shinkafar da ruwa ya lalata gonakinsu sun karbi bashi ne don noma shinkafar, ga shi ruwa ya lalata ta.

Malam Maigari ya yi kira ga gwamnatin jihar ta taimake musu da tallafi domin samun saukin radadin hasarar da  suka yi.