Ambaliya ta lalata gidaje 2,517 da hektar gonaki 1,000 a Gombe

Ya roƙi gwamnatin jihar da ta tarayya da su taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.

Ambaliya ta lalata gidaje 2,517 da hektar gonaki 1,000 a Gombe

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA), ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da shaguna 2,517 a yankuna 33 a jihar.

Mataimakin Daraktan Bayar da Tallafi na hukumar, Malam Ibrahim Nalado ne, ya bayyana hakan yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Asabar a Gombe.

Ya yi bayanin cewa ambaliyar ta shafi yankunan Ƙananan Hukumomin Dukku, Funakaye, da Billiri daga ranar 12 ga watan Agusta zuwa 22 ga watan Agusta sakamakon mamakon ruwan sama.

A cewarsa, “A Ƙaramar Hukumar Dukku, yankuna 10 ambaliyar ruwan ta shafa, a Ƙaramar Hukumar Funakaye yankuna 20 ta shafa, sannan a Ƙaramar Hukumar Billiri yankuna uku ne lamarin ya shafa.”

Ambaliyar ta fi lalata gidaje, amma duk da haka ta shafi gonaki a yankunan.

Sai sai babu wanda ya rasa ransa, amma yara biyu sun ji rauni a yankin Dukku, sannan dabbobi bakwai ruwa ya tafi da su.

Nalado, ya kuma bayyana cewa yankin Hina da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu/Deba ne, ya fi shan wahala wajen lalacewar gonaki, inda kimanin hektar 1,000 na gonakin shinkafa, masara, dawa, da gero duka ruwa ya shafe su.

Hukumar ta ziyarci yankin Hina a ranar 30 ga watan Agusta domin yadda ruwan ya yi ɓarna.

Ko da yake manoman yankin, sun damu matuƙa, inda suka buƙataci hukumomi su tallafa musu.

SEMA, na ci gaba da tattara bayanai kan manoman da abin ya shafa kuma za ta miƙa rahotonta ga gwamnatin jihar da sauran hukumomi da abin ya shafa.

Nalado, ya jaddada cewa akwai buƙatar samun taimakon gwamnatocin jiha da na Tarayya.

Kazalika, ya yi kira ga Hukumar Raya Arewa Maso Gabas (NEDC) da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da su taimaka.

Har wa yau, ya yi kira ga manoman da abin ya shafa da mazauna yankin da su yi haƙuri, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati da sauran hukumomi za su kawo musu ɗauki.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja