Ambaliya ta lalata gidaje kusan 150 a Jos
Ambaliyar ta biyo bayan ruwan da aka tafka a ranakun Asabar da Lahadi
Kusan gidaje 150 ne suka lalace sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita wasu unguwanni da ke Jos, babban birnin Jihar Filato.
Yankunan da ambaliyar ta shafa su ne Anguwan Rogo da Rikkos da Bauchi Road da kuma Naraguta, dukkansu a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.
- An lakada wa Kwamishina duka a wajen rabon kayan tallafi a Ondo
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Kasuwa Ke Neman Hana Kayan Abinci Sauka
Ambaliyar ta biyo bayan wani mamakon ruwa ne da aka tafka a ranakun Asabar da Lahadi.
Tanko Yakubu Alhassan, wani mazaunin titin Bauchi Road ya shaida wa manema labarai cewa mutanen da ambaliyar ta ɗaiɗaita yanzu haka sun samu mafaka a a gidajen ’yan uwa da abokan arziki.
Ya kuma ce, “Ba a samu asarar rai ba ko ɗaya, amma da yake ambaliyar ta yi yawa, sama da muhallai 150 ne suka lalace.”
Ita kuwa ɗaya daga cikin mutanen da lamarin ya shafa mai suna Salamatu Aliyu, cewa ya yi, “Ba ku taba tsammaninta ba. Mamakon ruwan saman ya shafi gidana da na makwabtana a Unguwar Rogo. Muna kira ga gwamnati da sauran masu hannu da shuni da su kawo mana ɗauki.”