Ambaliya ta raba dubban mutane da gidajensu a Maiduguri
Da talatainin dare ambaliyar ta mamaye tituna da gidaje da gadojin da sauran wurare
Dubban mutane sun bar gidajensu sakamakon gagarumar ambaliya a garin Maiduguri, fadar Jihar Borno.
Da talatainin dare ne ambaliyar ta mamaye Fadar Shehun Borno da tituna da gidaje da gadojin da sauran wurare, lamarin da ya tilasta wa jama’a sauya matsuguni.
Wasu majiyoyi sun ce an shekara kimanin 30 rabon da a ga irin wannan albaliya a garin Maiduguri
Wani shaida ya bayyana cewa a daren ne Madatsar Ruwa ta Alao Dam da ke kusa da garin Maiduguri ya fashe.
Ya ce ruwan ambaliyar ya yi ƙarfin gaske inda ya mamaye Fadar Shehun Borno, Kofa Biyu, Gadar Fori wadda ta haɗa Fori da Galtimari zuwa Tashan Bama.
- DSS ta sako Ajaero ’yan mintoci kafin cikar wa’adin NLC
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Magance Matsalolin Najeriya
- Ambaliya: Zulum ya rufe makarantu nan take
A cewarsa, unguwannin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Fori, Galtimari, Gwange, da Bulabulin.
“Kowa ya kaurace wa yankin post office, kasuwar Monday Market zuwa zoo da gidan man Hissan saboda ambaliya ta riga ta shanye su, mota ba ya iya bi,” in ji Refeal.
“Da mislain 12:30 aka sanar da mu cewa mu kwashe ’yan kananan kayan da za mu iya, amma kafin mu ciro takardun shaidar karatumu, har ruwan ya kawo mana mara,’ in ji wani mazaunin Galtimari.
Bilyaminu Yusuf, ya ce, “muna cikin mawuyacin hali a Lagos Street, ambaliya ta sa mu hijira zuwa makarantar Firamare ta Galtimari mun bar kayanmu a gida.”
Wakilinmu ya gano yadda ruwan ya shanye Gadar Lagos Street, daya daga cikin manyan gadojin da ke garin Maiduguri.
Hakazalika gidan radiyo da talabijin na jihar (BRTV) Post Office, Shehu Laminu way, da unguwar Custom su ma ambaliyar ta shafe su.
Wani ma’aikacin BRTV ya wallafa a Soshiyal Midiya cewa, “ruwa ya shanye ofishinmu da Post Office.”
Kimanin mako guda ke nan da ambaliyar ta yi ƙamari a jihar, inda lamarin ya kai maƙura a safiyar Talata.
Kazalika ambaliya ta mamaye wurare da dama a Ƙaramar Hukumar Jere ta jihar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe makarantun firamare da sakandare domin guje wa asarar rayukan dalibai a sakamakon ambaliyar.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne sakamakon rahoton da ke nuna yiwuwar ƙaruwar ambaliya a Maiduguri da Jere da wasu sassan jihar.