Ambaliya ta tilasta wa ango da amarya zuwa bikinsu a tukunyar girki
Sun karbi aron tukunyar girki don amfani da ita a matsayin kwalekwale don zuwa daurin aurensu.
An yada hotunan wani ango da amaryarsa zaune a cikin tukunyar girki a kan wani ruwa da ke ratsa tittunan da ambaliya ta shafa domin isa wajen bikinsu a gabashin kasar Indiya wanda hakan ya ja hankalin mutane.
Amarya da angon sun yanke shawarar isa wajen bikinsu ne ta wannan hanya sakamakon ambaliyar ruwa da ta malale ko’ina a yankinsu.
- Matashi yana neman wanda zai saye shi a Kano
- Barayin waya a kan Adaidaita Sahu sun hallaka matashi a Kano
Ma’auratan masu suna Akash da Aishwarya sun lashi takobin tabbatuwar aurensu duk da cewa, kauyensu na Thalabady a Jihar Kerala ya cika makil da ruwa a ranar Litinin da ta gabata.
Hotunansu da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna yadda ma’auratan biyu wadanda dukkansu ma’aikatan lafiya ne zaune a cikin tukunyar suna fara’a da annashuwa.
Ruwa kamar da bakin kwarya a yankin Kerala ya haifar da ambaliyar da ta yi sanadiyyar rasa rayuka da zabtarewar kasa.
Rafuka sun cika sun batse haka gadoji da manyan tittuna sun lalace – a wasu sassan kauyuka duk sun daidaita.
An tsara gudanar da bikin Akash da Aishwarya a wani karamin wajen bauta ne da ke Thalabady, sai dai ambaliyar ta shafi wani bangare na wajen taron bikin.
Amaryar da angonta sun aro tukunyar karfe ce daga wani karamin wajen bauta inda suka nemi taimakon wadansu maza su rika jan su har zuwa wajen bikin nasu.
“Wannan ya kasance bikin da ba za mu taba mantawa da shi ba,” inji amarya Aishwarya, lokacin da take tattaunawa da kafar labarai ta Asianet.
Sababbin ma’auratan sun ce, da farko sun tsara gudanar da bikinsu da karamin taron mutane, sai dai yanayin da bikin ya riske su da hotunan da aka rika yadawa a shafukan intanet komai ya sauya domin ranar ta kasance wadda ba za su taba mantawa da ita ba a tarihi.
Akash ya ce, sun dade da tsayar da ranar bikin nasu don haka ba za su dage ta ba, duk da cewa ta zo musu cikin mamakon ruwan sama, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na PTI ya ruwaito.
Angon ya kara da cewa tukunyar girkin ta kasance zabinsu na karshe don isa wajen bikin aurensu.