Ambaliya ta yi ajalin mutum 26, ta rusa gidaje 2,026 a Kano
Kimanin mutum 26 ne suka rasa rayukansu, da gidaje 2,026 da suka rushe
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da dukiya ta kimanin Naira biliyan 1.6 a wasu Kananan Hukumomi takwas na jihar.
Dokta Sale Jili, Babban Sakataren Hukumar ne ya bayyana haka yayin zanta wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a ranar Lahadi.
Jili ya ce Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta kasa NiMet ta yi hasashen aukuwar ambaliyar ruwa a Kananan Hukumomi 25 bisa la’akari da mamakon ruwan sama da ake tsammanin saukarsa a daminar bana.
“Kimanin mutum 26 ne suka rasa rayukansu, da gidaje 2,026 da suka rushe kari a kan gonakin shinkafa 95 da suka salwanta da kuma mutum 19 da suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa,” a cewarsa.
A cewarsa, Kananan Hukumomin da ambaliyar ruwan ta shafa sun hada da Bunkure, Minjibir, Tarauni, Doguwa, Rano Ungogo, Tsanyawa da Tudun Wada.
“Mun ziyarci Bunkure, Minjibir, Tarauni da kuma Doguwa domin rarraba kayan tallafi a wani yunkuri na rage radadin da mutane suka kansu a ciki.
“Daga cikin kayayyakin da muka rarraba akwai kayan abinci, buhunan siminti, rufin kwano, tabarmu da mayafan rufa,” in ji shi.
Ya kara da cewa, hukumar ta tura tawagar wasu jami’anta zuwa Karamar Hukumar Tudun Wada da ambaliyar ta fi shafa domin gano girman barnar da ta yi.