Ambaliya ta yi barna a jihohi 20, wasu 13 na cikin hadari

Akwai yiwuwar karuwar adadin jihohin da abin ya shafa zuwa 33 tsakanin watan Agusta zuwa Oktoba

Ambaliya ta yi barna a jihohi 20, wasu 13 na cikin hadari

Shugabar Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA), Zubaida Umar. (Hoto: X/TheZubaidaUmar)

Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana cewa, kananan hukumomi 52 a jihohi 20 ne ambaliya ta shafa.

Darakta-Janar na Hukumar, Zubaida Umar, ta ce akwai yiwuwar karuwar adadin jihohin da abin ya shafa zuwa 33 tsakanin watan Agusta zuwa Oktoba, bisa hasashen da Hukumar Kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi.

Da take magana a wani taron agajin gaggawa ta kasa a Abuja, Zubaida ta ce, kawo yanzu ambaliyar ta yi ajalin mutane uku.

Ta danganta raguwar adadin mace-macen da ake samu sda karuwar wayar da kan al’umma kan hanyoyin kauce wa mutuwa da hadari a lokacin ambaliya.

Dangane da sauya wa jama’a matsuguni daga wurare masu ambaliya, ta ce a jihohin Kebbi da Sokkwato, gwamnati ta yi nasarar sauya wa mutane wurin  zama zuwa kan tudu.

Ta kuma jaddada cewa an shawarci gwamnatocin jihohi da su ci gaba da tsugunar da jama’a a wuraren da suka fi aminci.

Zubaida Umar ta jaddada cewa hukumar NEMA ta sauya salon aikinta zuwa na kariya daga aukuwar abin da ake gudu, maimakon bari sai ya faru kafin a dauki mataki.

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji