Ambaliya: Tinubu ya umarci Shettima ya ziyarci Maiduguri

Tinubu ya jajanta wa al’ummar da ambaliyar ta shafa a Maiduguri.

Ambaliya: Tinubu ya umarci Shettima ya ziyarci Maiduguri

Shugaba Bola Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ya gaggauta ziyartar Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye garin.

Shettima ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin taron Hadar-Hadar Banki d Kuɗi na shekara 17.

Ya ce, “Bayan wannan taron, tare da izinin Shugaban Ƙasa, zan tafi Maiduguri. Birnin ya shiga mawuyacin hali sakamakon ambaliyar ruwa.

“Wannan matsala ba ta taƙaita ga wani yankin guda ba, muna fuskantar irin wannan a Bayelsa har zuwa Sakkwato.”

Ya tabbatar wa jama’a cewa Shugaba Tinubu ya damu game da halin da ake ciki kuma zai yi duk mai yiwuwa don taimakawa waɗanda lamarin ya shafa.

Haka kuma, Shettima ya miƙa ta’aziyyarsa a madadin gwamnatin Shugaba Tinubu ga dukkanin waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin ƙasar nan.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa mutane da dama sun rasa gidajensu a Maiduguri sakamakon ɓallewar madatsar ruwa ta Alau.

Ruwa ya mamaye gidaje, hanyoyi, da gadaje, lamarin da ya sa wasu wuraren a birnin ba sa shigowa.

Wakilin Aminiya ya zagaya cikin birnin, inda ya bayyana cewa ruwa ya mamaye wurare ciki har sa Fadar Shehun Borno, Kasuwar Maiduguri, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

Sauran wuraren da ambaliyar ta shafa sun haɗa, Gidan Adana Dabbobi da ke Maiduguri, Kwalejin Koyon Kiwon Lafiya, da sauransu.

Wasu daga mazauna garin sun fara kwashe kayansu zuwa wasu wurare domin neman mafaka.

Gwamnatin jihar ba ta fitar da alƙaluman waɗanda abin ya shafa ba, amma ta rufe makarantu na tsawon makonni biyu.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume