Ambaliya: WHO ta tallafa wa Borno da kayan rigakafin cututtuka 

Hukumar ta ce kayayyakin za su taimaka wajen daƙile cutar Kwalara da ke barazana ga waɗanda ambaliyar ta shafa.

Ambaliya: WHO ta tallafa wa Borno da kayan rigakafin cututtuka 

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta bai wa Gwamnatin Jihar Borno, tallafin kayan rigakafin cutar Kwalara domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

Jami’in hukumar mai kula da harkokin kiwon lafiya a jihar, Dokta Walter Kazadi Molumbo ne, ya gabatar da kayan tallafin a Maiduguri.

Tallafin ya haɗa da na’urorin gwajin cutar kwalara guda biyar, na’urorin SAM guda 14, da sauran kayayyakin jinya don ƙarfafa gwiwa ga gwamnatin jihar na ɗaukar matakan da suka dace wajen magance ambaliyar ruwa.

Ya ce, “Mun zo ne domin jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno da Iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa.

“Ambaliyar ta yi ɓarna wajen raba dubban mutane da gidajensu, yadda makarantu da asibitoci su ma suka nutse a wannan ambaliyar ruwa wadda akwai buƙatar kulawa cikin gaggawa.”

Wakilin hukumar, ya kuma bayyana cewa, na’urorin tantance cutar kwalara za su taka rawar gani wajen yin rigakafi da shawo kan ɓarkewar cutar.

Kazalika, ya ce kayayyakin SAM za su taimaka wa ma’aikatan kiwon lafiya wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a tsakanin yara, tare da ba su damar samun kyakkyawar makoma.

A cewarsa kowane ɗaya daga kayan gwajin na cutar kwalara zai iya ɗaukar gwajin mutum 100.

Har wa yau, na’urorin SAM guda 14 za su samar da muhimman kayayyakin jinya don kula da yaran da ke fuskantar matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

Ya gode wa Gwamnatin Jihar Borno bisa goyon baya da sadaukarwar da suke bayarwa wajen inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

Ya kuma yaba wa masu ruwa da tsaki abokan haɗin gwiwa da suke ba su gudunmawa wajen gudanar da ayyukansu.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu