Ambaliya Ta Tafi Da Hanyar Jirgin Kasa Daga Legas Zuwa Kano

An dage ranar dawowar sufurin jirgin kasa daga Legas zuwa Arewacin Najeriya.

Ambaliya Ta Tafi Da Hanyar Jirgin Kasa Daga Legas Zuwa Kano

Titin jirgin kasa. (Hoto: adobestock)


Ruwan sama ya lalata hanyar jirgin kasa a kudu maso yammacin Najeriya, lamarin da ya tilasta jinkirta farfado da zirga-zirgar jirgin kasa daga Legas zuwa Kano. 

A da dai da yammacin ranar Juma’a aka shirya dawowar zirga-zirgar.

Shirin Najeriya a Yau ya duba wannan lamari da ma muhimamncin dawo da sufurin jiragen kasar ga al’ummar Najeriya.