Ambaliya: Zulum ya raba kayan abinci a Ngala
Gwamnan ya raba kayan abincin don rage sa jama’a radaɗin ambaliyar ruwa.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da rabon kayan abinci kimanin tirela 100 ga mazauna Ƙaramar Hukumar Ngala, waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa na tsawon watanni huɗu.
Rahotanni sun nuna cewa, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da tallafin kayan abincin da aka bai wa Jihar Borno.
- Kashi 59 na mata na fuskantar cin zarafi a Gombe – Uwargidan Gwamna
- Rashin aiki ya ƙaru zuwa kashi 4.3 a Najeriya — Rahoto
Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya bayyana cewa an raba kayan ne a yankunan Gamboru, Ngala, da wasu ƙauyuka da suka fuskanci ambaliyar ruwa a watanni huɗun da suka gabata.
Kayan abincin da aka raba sun haɗa da masara, dawa, da gero, inda aka fi bai wa marasa fifiko yayin rabon.
Zulum ya ce, ’Mun fara rabon kayan abinci daga tirela 100 a Ƙaramar Hukumar Ngala.“
Ya ƙara da cewa, “Wannan yanki ya shafe kusan watanni huɗu ba tare da samun sauƙin shiga daga sauran sassan jihar ba, sakamakon ambaliyar ruwa.”
Gwamnan ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da hukumomin gwamnatin tarayya bisa tallafin da suka bayar don tallafa wa waɗanda iftila’in ambaliyar ya shafa.
Ya ce, “Shugaban Ƙasa ya ba mu tirela 100 na kayan abinci, ciki har da masara, gero, da dawa.
“Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta raba mana tirela 100 ta shinkafa domin tallafa wa mutanen Maiduguri da Ngala.”
Gwamna Zulum, ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ƙoƙarin rage dogaro da rabon kayan tallafi ta hanyar samar da ayyukan noma don mutanen yankin su riƙa dogaro da kansu.
Ya ce, “Mun ƙaddamar da shirye-shirye da za su taimaka wa mutane su koma noman rani da sauran ayyuka don inganta rayuwarsu.
“A Ƙaramar Hukumar Ngala, muna gina wuraren ban ruwa domin mutane su samu damar noma duk shekara.”