Ambaliyar Maiduguri: Al’ummar Yarbawa Na Neman Agaji

Kungiyar Yarabawa a Jihar Borno ta yi kira da a kawo mata dauki cikin gaggawa tare da tallafa musu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta shafi mambobinta akalla 4,600, da suka hada da  manyan masu sana’ar hannu da kuma masu fafutukar neman abin da za a ci. Shugaban kungiyar, Saka Ganiyu Abiodun ne, ya bayyana […]

Ambaliyar Maiduguri: Al’ummar Yarbawa Na Neman Agaji

Kungiyar Yarabawa a Jihar Borno ta yi kira da a kawo mata dauki cikin gaggawa tare da tallafa musu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta shafi mambobinta akalla 4,600, da suka hada da  manyan masu sana’ar hannu da kuma masu fafutukar neman abin da za a ci.

Shugaban kungiyar, Saka Ganiyu Abiodun ne, ya bayyana cewa bala’in ambaliyar ta dukiyoyi da abin dogaronsu, yana mai cewa waɗanda abin ya shafa sun yi asarar duk abin da suka mallaka.

Ya kuma jinjina wa kokarin gwamnatin jihar na gaggauta daukar matakan da suka dace tare da samar da wasu hanyoyin da za su taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa.

“A yanzu haka, muna da jerin sunayen mutane 4,600 da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa kuma akasarin mutanen masu sana’o’in hannunda ’yan kasuwa ne.

“Muna fuskantar wahalar samun kayan abinci, ruwa mai tsafta, da matsuguni; al’ummar mu da aka san ta da juriya, tana gab da rugujewa.

“Mutanenmu sun yi asarar komai, a gaskiya yawancinsu ba su da komai sai kayan da suke sanye da su.”

“Ambaliyar ta yi mummunar illa ga yankunan Kwastam, London Ciki, Rawan Sanfi, Gidan-Danbe da Gomboru waɗanda galibin mutanenmu suke zaune.” in ji shi.

Saka ya roki daidaikun mutane, kungiyoyi masu ba da tallafi na cikin gida da ba waje da hukumomin gwamnati da su kawo musu agaji akan lokaci.

“Ana buƙatar gudummawar kuɗi don sake gina gidaje da suka lalace da tallafa wa iyalai waɗanda suka rasa komai.” In ji Saka.