Ambaliyar Maiduguri: Ruwa ya tono gawarwaki, mutane 200,000 sun rasa gidajensu
Majinyata sun maƙale, ƙananan yara sun ɓace, ana fargabar harin kadoji
Ruwa ya tono gawarwaki daga maƙabarta, mutane da dama kuma su ɓace ciki har da ƙananan yara a sakamakon Ambaliyar Maiduguri a Jihar Borno.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta ce sama da mutane 200,000 ne suka rasa gidajensu a sakamakon ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a Jihar Borno a shekaru 30 da suka gabata.
Marasa lafiya sun maƙale a yayin da ruwan ya shanye asibiti da gidaje da wuraren kasuwanci da gadoji.
Mutane na zulllumin yiwuwar harin macizai da kadoji bayan ruwan ya yi da su daga gidan Zoo.
- DAGA LARABA: Ribar Da ’Yan Najeriya Za Su Samu Daga Hulda Da China
- Ambaliya: Al’amura sun munana a Borno — SEMA
Yiyuwar ruwa ya ci yara
Har yanzu ba a ga mutane da dama da suka ɓace ba, ciki har ka ƙanana da yara.
Yawancin mazauna garin da suka zanta da Aminiya bayan ambaliyar sun ce ba su iya gano ’yan uwansu ba.
Wasu majiyoyi a yankin Gwange sun ce akwai yiwuwar yara da dama sun nutse a ruwan.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Za ka yi ta ganin wasu iyaye mata suna kuka, suna neman ’ya’yansu.”
Wata mata mai suna Ya’ana ta ce: “Maƙwabtana ne suka tashe ni da misalin karfe 3:30 na asuba.
“Na firgita sa’ad da na ga ruwa na kwarara cikin gidanmu. Na yi ƙoƙarin ceto ’ya’yana daga nutsewa, amma har yanzu ban ga biyu daga cikinsu ba.”
Fatima Ali, ta ce: “Na samu na tsira, amma mahaifana da ’yan uwana shida sun maƙale.
“Ina roƙon gwamnati ta yi duk mai yiwuwa ta ceto su.”
Gawarwaki a kan tituna
Haka kuma ruwan ya shanye Maƙabartar Gwange da ke Maiduguri, lamarin da ya sa gawarwaki ke shawagi a kan tituna.
Wani mazaunin garin ya ce: “Ruwan ya riga ya shanye makabartar, ya ciro gawarwaki daga wasu kaburbura.
“Mata da yara suna cikin damuwa saboda munanan abubuwan gani.”
Majinyata sun maƙale a asibiti
Haka kuma da yawa daga cikin majinyata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) sun maƙale yayin da wurin ya shanye harabar.
Ali Galadima, wanda aka kwantar da matarsa a UMTH, ya ce an kwashe marasa lafiya a hawa na saman bene, saboda ruwa ya shanye hawan farko na benen.
“Tana kukan yunwa amma ruwan ya hana ni shiga asibiti. Dangin marasa lafiya da yawa sun maƙale suna neman hanyoyin shiga wurin, ”in ji shi.
Asarar kadarori
Ambaliyar ta lalata kadarori da dama da suka hada da gidaje da gonaki da wuraren kasuwanci.
Ambaliyar ta tilasta wa mutane da dama barin gidajenau, akasarinsu a Ƙaramar Hukumar Jere ne, an tilasta musu barin gidajensu.
Ibtila’in ya biyo bayan rugujewar Madatsar Ruwa ta Alau, mai nisan kimanin kilomita 10 zuwa cikin babban birnin jihar.
Ruwan ya shanye matsugunai da wuraren kasuwanci, ciki har da shahararriyar Kasuwar Monday da dubban gidaje da kadarori kamar Fadar Shehun Borno.
Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Shehuri, Gwange, Adamkolo, Gamboru, Fori, Bulabulin, yankunan gidan waya, Moromoro, da Gadar Kwastam da dai sauransu.
Wasu mazauna da suka zanta da wakilinmu sun ce rabon a samu irin wannan ambaliya da ta mamaye Maiduguri da kewaye ya kai shekaru 30.
Barazanar harin namun daji
Wani ɗan kasuwa mai suna Ibrahim Musa, ya ce: “Duk mun tashi daga yankin Gidan Zoo saboda guje wa hari daga namun dajin d ake tserewa.
“Sannan duk shagunan da ke yankin Kasuwar Monday ruwan ya shiga cikinsu.”
Amma Janar-Manaja na Gandun Dajin Sanda Kyarimi da ke Maiduguri, Ali Abatcha, ya ce ruwan ya tafi da macizai da kadoji zuwa cikin al’umma.
Don haka ya shawarci jama’a da su kasance sun hattara.
Amma ya ce kashi 80 na namun dajin wurin sun mutu a ambaliyar.
’Yan Kasuwar Monday sun tafka asara
Wani Mai sayar da sukari a Kasuwar Monday, Muhammad Bulama ya ce: “Kayanmu na biliyoyin Naira sun jike sun lalace. Sai addu’a kawai!”
Sauyin yanayi
Ibrahim Jirgi, wakilin BBC da Daily Times wanda ya ba da rahoton ambaliyar 1994 Maiduguri ya alaƙanta ambaliyar bana da sauyin yanayi.
“A 1994 gaba dayan Maiduguri ruwa ya shanye. Saman bishiyoyi mutane suka rika hawa domin tsira, yadda ka san alkiyama tabtsaya,” in ji shi.
Shirin ko-ta-kwana
Jami’in hukumar NEMA, Sirajo Garba, ya ce suna cikin shirin ko-ta-kwana a Maiduguri domin aikin ceto, amma bai ba da alƙaluman asarar rai ba.
Barazanar lafiya
Shugaban Kungiyar Likitoci Masu neman Kwarewa ta Kasa (NARD) reshen Jihar Borno, Abubakar Ngubdo, ya ce akwai barazanar barkewar cututtukan da gurbataccen ruwa ke yaɗawa, sakamakon gawarakin da ruwa ke yawo da su a ambaliyar.
“Hakazalika ruwan sokawe da wuraren zubar da shara da sauransu da ruwan ya shanye.
“Ya mamata gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakan kare yaɗuwar cutuka irin su amai da gudawa da Taifod sannan a samar da nagartaccen matsugu da ruwan sha da makewayi da magunguna ga masu gudun hijira.
“Mutanen da suka nuna alamar rashin lafiya kuma a gaggauta ba su kulawar da ta dace.”
An buɗe sansanin gudun hijira
Tuni dai Gwamnatin Borno ta bude sansanoni domin tsugunar da jama’an da suka rasa gidajensu.
An fara yi wa mutane rajista tun ranar Talata tare da kira gare su da guji zama wuraren za su iya kasancewa hanyar ruwa.