TY Danjuma Ya Bayar da Tallafin N1bn Kan Ambaliyar Maiduguri

Janar T Y Danjuma Janar Danjuma ya nuna damuwa kan halin da mutanen abin ya shafa suka shiga

TY Danjuma Ya Bayar da Tallafin N1bn Kan Ambaliyar Maiduguri

Janar Theophilus Yakubu Danjuma (murabus) ya bayar da gudummawar Naira biliyan guda domin tallafa wa mutanen da bala’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

Ambaliyar ta raba dubban mutane da muhallansu tare haddasa gagaruwar asarar dukiyoyi da gidaje da ababen more rayuwa, lamarin da ya sa mutane da dama ke bukatar agajin gaggawa.

Da yake mika gudummawar tasa ga gwamnatin Jihar Borno, Janar Danjuma ya nuna damuwa kan halin da mutanen abin ya shafa suka shiga, yana mai jaddada mahimmancin tallafa wa duk wadanda suke cikin a irin wannan hali.

“Abin da ya faru a Maiduguri halin da halin da wadanda abin ya shafa suka shiga na matukar damu na; akwai muhimmanci sosai a tallafa wa al’umma.

“Wannan gudummawar, ina tsammanin za ta taimaka wajen samar da agajin gaggawa, ciki har da matsuguni, abinci, da taimakon magunguna ga waɗanda abin ya shafa,” in ji shi.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7