Ambaliyar Ruwa: Ana ci gaba da aikin ceto a Amurka
Ana ci gaba da aikin ceto a Jihar Tedas da Oklahoma da kuma wurare daban-daban sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya. Rahotanni sun bayyana cewa mutane 10 ne suka mutu sakamakon wa nan ambaliyar wanda akayi a ranar Litinin da ta gabata, inda ta kai har wayewar […]
Ana ci gaba da aikin ceto a Jihar Tedas da Oklahoma da kuma wurare daban-daban sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane 10 ne suka mutu sakamakon wa nan ambaliyar wanda akayi a ranar Litinin da ta gabata, inda ta kai har wayewar garin Talata.
Baya ga rayuka da dukiya da ambaliyar ta salwantar, wasu hanyoyi ba a bi ta kansu haka kuma wasu gidaje wannan ambaliyan ta yi gaba da su, wannan ya sa aka yi watsi da wasu ababen hawa da iftilayin ya rutsa da su.
Magajin garin Houston Anise Parker ya ce da zaran lamarin ya natsa ma’aikatar ceto za su fara aiki ka-in-da-na-in domin ganin sun agaza wajen gyara wasu hanyoyi tare da kawar da wasu abubuwa da ambaliyar ta sa suka yi wa tituna shinge.
Sai dai kuma ya bayyana shakunsa game da lokacin da za su fara wannan aikin domin manazarta sun ce ga bisa dukkan alamu za a ci gaba da wannan ruwan har tsawon wannan makon.