Ambaliyar ruwa: Bayelsa ta roki a kawo dauki ta jiragen sama

Ruwa ya shanye rabin jihar da hanyoyin da suka hada ta da makwabta

Ambaliyar ruwa: Bayelsa ta roki a kawo dauki ta jiragen sama

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kawo dauki Bayelsa ta sama don ceto al’ummar jihar daga ambaliyar ruwa.

Kiran ya fito ne daga tsohon gwamnan jihar kuma a yanzu sanatan Bayelsa ta Yamma, Henry Seriake Dickson.

Sanatan ya yi kiran ne da babbar murya ga Shugaba Buhari na kawo daukin gaggawa ta sama don kubuto mutanen da ambaliyar ruwa ya rutsa da su.

Sierake Dickson na cewa yin haka cikin gaggawa zai rage yawan asarar rayuka na wadanda ambaliyar ta rutsa da su a muhallinsu.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kai dauki gaggawa na kayayyakin bukatu da kuma magunguna zuwa jihar.

Tsohon gwamnan ya yi kira gare ta da ta aiko da sojoji da sauran masu aikin damara su kawo dauki don magance ambaliyar.

Su kuma taimaka wajen samar da sansanoni kula da wadanda suka jikkata, da kuma bayar da magunguna a kasancewar kusan rabin dayanta ruwa ya shafe ta.

Tsohon gwamnan yana magana ne dogaro da yadda ya gamu da irin wannan ambaliyar a shekarun 2012 da 2016 da kuma 2020 a lokacin yana mulki.

Wakilinmu ya rawaito cewa, daukacin manyan hanyoyin da suka hada jihar da makwabta ruwa ya shafe su, wanda ya katse jihar da ko’ina a kasar nan, ya kuma rutsa al’ummu da yawa.