Ambaliyar Ruwa: Kungiya ta nesanta kanta daga zargin Gwamnatin Kano

Ambaliyar ruwan na da alaka da filayen da gwamnatin ta cefanar kuma aka yi gine-gine a cikinsu.

Ambaliyar Ruwa: Kungiya ta nesanta kanta daga zargin Gwamnatin Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano

Wata Kungiyar Ci gaban Unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, ta nesanta kanta daga wata sanarwa da wata kungiyar dalibai a unguwar ta fitar tana dora alhakin ambaliyar ruwa da rushewar gidaje a kan gwamnatin jihar.

Uwar kungiyar ta IKMA wacce kungiyar daliban ta ke karkashi, ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar wacce ta fitar da sa hannun dukkannin shugabanninta, ta ce ba da yawunta kungiyar daliban ta zargi gwamnatin jihar ba, lamarin da ta ce ta nesanta kanta da shi.

“Kungiyar Inuwar Unguwar Kofar Mata tana da kyakkyawar fahimta tsakaninta da gwamnatin Jihar Kano da kuma Masarautar Kano”.

“Saboda haka sha’anin ambaliyar ruwa ba Kofar Mata kadai ya shafa ba, kusan lamari ne da ya shafi sassa daban-daban na kasar nan, kuma kungiyar na daukar matakan dakile afkuwar lamarin a nan gaba.”

A ranar Talata ce kungiyar daliban ta fitar da wata sanarwar tana mai dora wa Gwamnatin Kano laifi dangane da ambliyar ruwan da ta haddasa rushewar gidaje a unguwar.

Kungiyar daliban ta yi zargin cewa ambaliyar ruwan na da alaka ne da filayen da gwamnatin ta cefanar kuma aka yi gine-gine a cikinsu ciki har da wanda jama’ar unguwar ke zubar da shara. 

Daliban dai sun yi koken ne kan abin da suka kira mahukuntan da suka dace su dauki mataki kan lamari sun yi watsi da su.

Kazalika, sun yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kawo dauki.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara