Ambaliyar ruwa: Rigakafi ya fi magani 

A bara an samu ambaliyar ruwa wacce ta rushe gidajen talakawa ta lakume gonaki, a wasu wuraren ma har da asarar rayuka. Ba za mu ce ba a ba wa al’umma tallafi ba, amma ya yi kadan, a wasu wuraren kuma tallafin ma bai isa ga wadanda aka ba da dominsu ba. Sannan tambayata ita […]

Ambaliyar ruwa: Rigakafi ya fi magani 
Ambaliyar ruwa: Rigakafi ya fi magani 

A bara an samu ambaliyar ruwa wacce ta rushe gidajen talakawa ta lakume gonaki, a wasu wuraren ma har da asarar rayuka. Ba za mu ce ba a ba wa al’umma tallafi ba, amma ya yi kadan, a wasu wuraren kuma tallafin ma bai isa ga wadanda aka ba da dominsu ba. Sannan tambayata ita ce a gwamnatance wane mataki aka dauka domin kauce wa ambaliyar irin wacce ta faru a barar?

Akwai bukatar wasu wuraren a canja wa al’umma matsugunni domin su ba ruwa hanyarsa, wasu wuraren kuma ana bukatar a gyara magudanun ruwa da ko dai suka rushe ko kuma suka toshe saboda jibgin sharar da ake zubawa a ciki. Sannan a wasu wuraren kuma gonaki ya kamata a gina madatsun ruwan. Akwai matakai da dama da suka kamata a dauka don kawar da ambaliyar ruwa ko kuma rage kaifin asarar da ake yi duk shekara, amma an kasa dauka.

Gwamnoni kai ka ce sun fi son bala’in ya faru domin su kan fid da kudi da sunan taimaka wa talakawa, kuma manyan attajirai su ba da tallafi, Gwamnatin Tarayya ma ta ba da nata tallafin, amma a karshe talakawan da bala’in ya shafa sai su bi su da Naira dubu biyar-biyar. A mafi yawan lokaci in an samu ambaliya akan raba wa jama’a bargo da buta ne kawai. Don haka ya kamata hukumomin da suke da hakki a kan kula da ambaliyar ruwa su sani cewa rigakafi fa ya fi magani.

Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688)