Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a Gombe
Al’ummar yankin ta nemi gwamnati ta tallafa musu.
Mazauna ƙauyen Wuro Dole da ke Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe, na cikin damuwa bayan da ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, gonaki, amfanin gona da kuma dabbobi.
Ambaliyar ta faru ne bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a yankin, lamarin da ya sa iyalai da dama suka rasa matsugunansu da hanyoyin samun abinci.
- Sojoji sun cafke shugaban ’yan bindiga a Zamfara
- Masu kai wa Boko Haram bayanai sun shiga hannu a Yobe
Shugaban Ƙaramar Hukumar Akko, Abdullahi Abdulkadir, ya kai ziyara ƙauyen domin duba irin barnar da ambaliyar ta yi.
Ya jajanta wa al’ummar da abin ya shafa tare da tabbatar musu cewa gwamnati za ta taimaka musu.
Ya ce za a tantance asarar da aka yi domin a samar da tallafin da ya dace ga waɗanda abin ya shafa.
Hakimin ƙauyen, Hussaini Ishiyaku, ya yaba da ziyarar jami’an gwamnati, sannan ya roƙi gwamnati da ƙungiyoyin agaji da su kawo wa al’ummar yankin ɗauki cikin gaggawa.
Shi ma ɗan majalisar dokokin Jihar Gombe mai wakiltar Akko ta Arewa, Musa Mohammed Wuro Biriji, ya bayar da tallafin Naira 250,000 ga waɗanda ambaliyar ta shafa, tare da alƙawarin neman ƙarin tallafi daga gwamnati.
Wasu mazauna ƙauyen sun ce ruwan sama mai ƙarfi da toshewar hanyoyin ruwa ne suka haddasa ambaliyar.
Sun bayyana cewa gidaje da dama sun rushe, yayin da gonaki da amfanin gona suka lalace.
Al’ummar Wuro Dole sun yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka musu.