Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gonaki a Jigawa
Ambaliyar ta lalata gonaki aƙala hekta 60 a yankin.
Mamakon ruwan sama da aka sake tafkawa ya haddasa ambaliya, inda ya lalata gonaki aƙalla hekta 60 a kauyukan Tashena da Arki da ke ƙaramar hukumar Malam-Madori a Jihar Jigawa.
Gonakin da ambaliyar ta shafa amfanin gonar irin su shinkafa da masara sun girma sosai.
- Gwamnati ta ayyana ɓarkewar cutar ƙyandar biri a Najeriya
- Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 2 a Zamfara
Manoma irin su Alhaji Haruna, wanda ya rasa hekta biyu na gonar masara, sun tafka asara mai tarin yawa.
Ambaliyar ta kuma shafi gonaki a ƙauyukan Matsa da Agin, inda ta lalata ƙarin gonakin shinkafa da masara.
Shugabannin al’umma, kamar Malam Yunusah Bulama, mai unguwar Tashena, suna ƙoƙarin tattara sunayen manoman da lamarin ya shafa domin neman agajin gaggawa.
Ambaliyar ta yi matuƙar illa ga harkar noma a yankin, inda manoma da dama suka rasa amfanin gonar da suka yi fatan za su girba tare da samun riba.