Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki dubu 3 da gidaje 120 a Jigawa
Ambaliya ruwa ta lalata sama da gonaki dubu 3 da kimanin gidaje 120 a garin Zugo da ke Karamar Hukumar Guri a jihar Jigawa. Jami’in watsa labarai na Karamar Hukumar Alhaji Sanusi Doro, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin dillacin Labarai NAN a Guri yau Alhamis. Alhaji Sanusi, ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta […]
Ambaliyar ruwa
Ambaliya ruwa ta lalata sama da gonaki dubu 3 da kimanin gidaje 120 a garin Zugo da ke Karamar Hukumar Guri a jihar Jigawa.
Jami’in watsa labarai na Karamar Hukumar Alhaji Sanusi Doro, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin dillacin Labarai NAN a Guri yau Alhamis.
Alhaji Sanusi, ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta mamaye hanyar Una-Zugobia wanda take babbar hanya ce da jama’a suke wucewa da amfanin gonakin su zuwa kasuwanni.
Ya kuma bukaci gwamnatin jihar da Hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) da ta tallafawa wadanda ambaliyar ta shafa da abinci da kuma magunguna.