Ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da tituna a Legas
Yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da: Epe da Eredo da Bogije da Labora da Abijon da Sangotedo da Awoyaya da Ibeju zuwa Lekki.
Ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanni da manyan tituna a sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ke kwarara a yankin Ibeju zuwa Lekki na Jihar Legas.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an kwashe sa’o’i ana ruwan a wannan Larabar a unguwannin da ke Ibeju zuwa Lekki da sauran unguwanni.
- Za a ƙirƙiro ƙarin jiha ɗaya a Nijeriya
- Majalisa ta kori kudurin hana hafsoshin tsaro karkatar da kudade
Wasu daga cikin yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da: Epe da Eredo da Bogije da Labora da Abijon da Sangotedo da Awoyaya da Ibeju zuwa Lekki.
Daga cikin mazauna unguwar da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, sun danganta ambaliyar da toshewar magudanan ruwa sakamakon zubar da shara da ake yi na gaira ba dalili.
Mista Rasheed Ayobami, wani mazaunin unguwar Labora da ke Ibeju-Lekki, ya ce gidansa wanda ya cika da ruwa maƙil ya rushe a dalilin ambaliyar, la’akari da cewa babu magudanar ruwa a yankunan unguwar da ya ke zaune.
“Akwai ruwa da yawa da ke kwarara cikin harabar gidana, duk gidan ya nutse.”
Wani mazaunin garin, Seyi Arowosaye, ya koka kan yadda ake yawan samun ambaliyar ruwa a babbar hanyar Ibeju zuwa Lekki sakamakon toshewar magudanan ruwa a cikin babban birnin.
Arowosaye ya yi kira ga mahukuntan Ƙaramar Hukumar Ibeju-Lekki da su share magudanun ruwa sannan ya buƙaci mazauna yankin da su daina zubar da shara a magudanan ruwan domin daƙile aukuwar hakan nan gaba.
Ya kuma buƙaci gwamnatin Jihar Legas da ta gaggauta kammala gyaran titunan yankin Sangotedo da ke Ibeju.
Wata mai suna Madam Bola Fadugba ta koka da yadda ruwan saman ya yi sanadiyyar ambaliya a yankin Labara.
“Ina zaune a Labara amma a lokacin damina nakan ƙaura da iyalina mu koma gidan ƙanwata da ke unguwar Eputu.
“A yanzu ambaliyar ruwa ta mamaye gidana saboda rashin magudanar ruwa a unguwar.