Ambaliyar ruwa ta rusa gadar da ta haɗa garuruwa 5 a Kebbi

Gadar ta ruguje ta haɗe ƙauyuka biyar a Jihar Kebbi.

Ambaliyar ruwa ta rusa gadar da ta haɗa garuruwa 5 a Kebbi

Ambaliyar ruwa

Ambaliya a sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya sauka tun daga daren ranar Alhamis har zuwa ranar Juma’a da rana ta ruguje wata gada a Ƙaramar Hukumar Maiyama ta Jihar Kebbi.

Rahotanni daga yankin na cewa, gadar ta haɗa ƙauyukan Mayalo da Sambawa da Gumbin-Kure da Unguwar Shuaibu, da kuma Gandiji.

Wani mazaunin yankin ya ce gadar babbar hanyar sufuri ce da ke zaman mahaɗar unguwanni kuma rugujewar ta ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da mu’amalar jama’a da samun muhimman ayyuka a ƙauyukan da abin ya shafa da kuma kewayensu.

Wani jami’in ƙaramar hukumar da ke yankin ya shaida wa wakilinmu cewa hukumomi sun fara aikin bayar da agaji.

“Tuni dai suka kwashe mutanen da suka maƙale a matsugunansu a yankunan da lamarin ya shafa.

“Suna kuma ci gaba tattara bayanai da tantance barnar da rugujewar da ta yi,” in ji shi.

Mazauna unguwannin da abin ya shafa sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta gyara gadar domin samun damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum a yankin.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki