Ambaliyar ruwa ta shafe hanyar Jigawa zuwa Bauchi da Gombe
Gwamnatin ta gargaɗi direbobi da su gujewa bin hanyar.
Babbar hanyar da ta haɗa Birninkudu, Malawa, Babaldu da jihohin Gombe da Bauchi a Jihar Jigawa, ta cika da ruwa, lamarin da haifar da tsaikon zirga-zirgar ababen hawa.
Hukumar Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Jigawa, ta gargaɗi direbobi da su guji bin hanyar.
- Shin jirgin ruwa ya nutse da ’yan bindiga 200 a Sakkwato?
- Zanga-zanga: ’Yan Sanda sun cafke mutum 873 a Kano
Wasu jama’a sun ce ruwan ya cika hanyar sosai ta yadda mutane ba sa iya amfani da hanyar.
Jami’in hukumar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud ya ce, “Lamarin ya yi ƙamari. Muna roƙon direbobi da su kula sosai kuma su bi wasu hanyoyi daban don kare lafiyarsu.”
Hukumar ta tura jami’anta yankin don su taimaka wa jama’a da suka maƙale a hanyar.
Ambaliyar ta shafi wasu yankuna da ke kusa da hanyar, inda mazauna yankin suka ce ruwa ya mamaye gidaje da gonakinsu.
Gwamnatin Jihar Jigawa, ta tabbatar wa da mazauna yankin cewa tana ɗaukar matakan rage illolin ambaliyar da kuma taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa.
Gwamnatin ta shawarci direbobi da su saurari bayanan hukumomi sannan su ɗauki duk matakan da suka dace don kare kansu daga ambaliyar.