Ambaliyar ruwa ta shafe maƙabarta a Kaduna

Ambaliyar ta faru ne sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi a ranar Litinin.

Ambaliyar ruwa ta shafe maƙabarta a Kaduna

Mazauna unguwar Chikaji da ke Ƙaramar Hukumar Sabongari a Jihar Kaduna, sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta kai musu agaji biyo bayan yadda ambaliyar ruwa ta shafe maƙabartar Hayin-Ojo.

Wannan kiran ya biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya jawo ambaliyar ruwa a safiyar Litinin.

Ambaliyar ta fi shafar yankin da ke kusa da magudanar ruwa daga Yan-awaki kusa da zagayen Kano zuwa Chikaji har zuwa Dam ɗin Shika a Sabon Gari.

Dagacin Chikaji, Alhaji Auwal Sani-Danbaba, ya shaida wa manema labarai cewa ambaliyar ta lalata gidaje sama da 200.

Kazalika, ta shafe wani ɓangare na Makarantar Firamare ta LEA da kuma wani ɓangare na Makabartar Hayin Ojo.

Ƙaburbura da dama sun buɗe, sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.

Amma ba a samu rahoton asarar rayuka ba.

Danbaba, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan rashin samun ɗauki ko agaji daga gwamnati ko wata hukuma.

Ya jaddada buƙatar gaggawar ɗaukar mataki daga hukumomin da ke kula da lamarin da ya shafi Iftila’in ambaliyar ruwa a jihar.

Suleiman Liman, babban limamin Masallacin Chikaji, ya bayyana cewar sun kira wani taron gaggawa na masu hannu da shuni domin magance matsalar da ta shagi maƙabartar da kuma taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.

Wani mutum da ambaliyar ta shafa ya ce yayin da suke ƙoƙarin kwashe ruwan da ya shiga gidansu, wani ɓangare na ginin gidan ya rushe.

Ya ce babbar damuwarsu shi ne yadda za su kare ‘ya’yansu daga baraguzan ginin.

Ya roƙi tallafi da gaggawar ɗaukar mataki daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Aminiya ta gano cewa yawancin waɗanda ambaliyar ta shafa suna zaune ne tare da ‘yan uwansu, yayin da wasu matan aure suka koma gidajen iyayensu har zuwa lokacin al’amura za su daidaita.

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur