Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum uku a Myanmar
Wata mazauniyar ƙauyen Kyauk Kyat, May Thein Yaine, ta ce daga cikin gidaje kusan 200 da ke ƙauyensu, guda ɗaya ko biyu ne kawai ba su nutse cikin ruwa ba.
Residents wade through floodwaters in Kyauktaw, Myanmar’s western Rakhine state on July 10, 2026. (Photo by AFP)
Masu aikin ceto a ƙasar Myanmar sun yi gargaɗin cewa ruwan sama na ci gaba da kwarara yayin da ambaliyar ruwa ke ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a jihohin Rakhine da Chin da ke yammacin ƙasar.
Ya zuwa yanzu dai aƙalla mutum uku ne suka mutu sakamakon ambaliyar, kamar yadda sabbin alƙaluman da sashen ayyukan jin ƙai na ƙungiyar Arakan Army mai iko da yankunan da bala’in ya fi shafa ta fitar suka nuna.
- Harin Rasha ya jikkata mutum 11 a Kyiv — Zelensky
- An kashe jami’an tsaro biyu a arewa maso gabashin Iran
Wani mai aikin ceto a ƙauyen She Ta Lay da ke Ƙaramar Hukumar Kyauktaw, Bo Aung Thein, ya ce babban abin da ke damunsu shi ne akwai yiwuwar ruwa ya ci gaba da kwarara.
A cewarsa, babban tashin hankalin da za su fuskanta shi ne samar wa masu rauni mafaka, musamman wajen kwashe tsofaffi, marasa lafiya, mata masu juna biyu da kuma mutanen da ke zaune a ƙananan wurare.
Tun bayan juyin mulkin soji da aka yi a shekarar 2021, Myanmar take fama da yaƙin basasa, wanda ya janyo matsalolin sufuri da sadarwa, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da kashi ɗaya bisa uku na al’ummar ƙasar na fama da ƙarancin abinci.
Wata mazauniyar ƙauyen Kyauk Kyat, May Thein Yaine, ta ce daga cikin gidaje kusan 200 da ke ƙauyensu, guda ɗaya ko biyu ne kawai ba su nutse cikin ruwa ba.
“Ruwan ya mamaye sauran gidajen, haka kuma ya mamaye duk gonakin shinkafa,” in ji ta.
Ita ma wata mazauniyar yankin mai shekara 24, Thuzar Aye, ta bayyana fargabar da take ciki.
“Muna da ƙananan yara a gida. Ina tsoron idan ruwan ya sake sauka da daddare, ba za mu sami wurin mafaka ko hanyar tserewa ba,” in ji ta.