Ambaliyar ruwa za ta ci gaba da muni gwargwadon sare itatuwa da ake yi – Dokta Kabir ‘Yammama

Matasalar ambaliyar ruwa ta haddasa asarar amfanin gona a wasu sassan kasar nan baya ga salwantar rayukan jama’a da muhalli a daminar bana, inda masana suka danganta lamarin da sauyin yanayi. Aminiya ta zanta da Dokta Kabir Abdulkadir ‘Yammama shugaban wata kungiya ta yaki da gusowar hamada inda ya yi hasashen cewa matsalar ka iya […]

Ambaliyar ruwa za ta ci gaba da muni gwargwadon sare itatuwa da ake yi – Dokta Kabir ‘Yammama

Dokta Kabir Abdulqadir ’Yammama

Matasalar ambaliyar ruwa ta haddasa asarar amfanin gona a wasu sassan kasar nan baya ga salwantar rayukan jama’a da muhalli a daminar bana, inda masana suka danganta lamarin da sauyin yanayi. Aminiya ta zanta da Dokta Kabir Abdulkadir ‘Yammama shugaban wata kungiya ta yaki da gusowar hamada inda ya yi hasashen cewa matsalar ka iya kara muni duk shekara, sannan ya yi bayani a kan yadda za a magance ta.

 

Aminiya: Mene ne tarihin wannan kungiya kuma wadanne ayyuka take aiwatarwa?

Dokta ’Yammama: An kafa kungiyar ce don yaki da gusowar hamada da kuma alkinta tattalin arzikin al’ummar karkara musamman na Arewa inda nan ne aka fi fama da wannar matsala. Uban kungiyarmu shi ne, tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Tarayya, Mai shari’a Umaru Abdullahi. Muna gudanar da ayyukanmu ne ta hanyar shirya gangami musamman a kauyuka da fadakar da su a kan tasirin amfanin dasa itatuwa da yadda za su kara amfana daga abubuwan da ke kewaye da su. Noma da kiwo su ne manyan abubuwa da al’ummarmu ke tinkaho da su kuma gaba dayansu sun ta’allaka ne a kan kasa, to ta yaya za mu tarairayi kasar nan don ci gaba da amfana da hakan da kuma kawar da fitinar gusowar hamada ko zaizayar kasa, wanda al’amari ne na ko mu kawar da shi ko kuma shi ya kawar da mu kamar yadda ya watsar da dabbobin daji ya kora makiyaya. To a kwana a tashi idan ba an tsaya ba zai kuma kawar da manoma sannan har ya zo kan wadanda ke amfani da kasar don gina gidaje ko tituna wanda tuni su ma ya fara shafarsu. Haka nan muna sanar da jama’a dabarun zamani na samar da makamashin girki don rage matsalar sare itatuwan da ake da su, da kuma yadda za su inganta abubuwan da suka noma don ba su gwaggwabar riba  maimakon sayar da shi haka nan, inda hakan zai samar da karin aikin yi ga al’ummarmu maimakon zama ana jiran wata daminar. Dalilin kafa ta ya biyo bayan gano halin da dazuzzukanmu masu tarihi ne suke ciki kamar dajin Falgore da na Rugu inda na samu shigarsu a lokacin da aka ba ni lasisin yin allurar rigakafi don yakar ciwon bushiya. Daga baya a lokacin Shugaban Kasa Abdulsalami Abubakar na rubuta takarda na gabatar masa don ankarar da Gwamnatin Tarayya kan fitinar da ke tafe, kuma a dalilin hakan ya ba ni damar in fadada abin sannan in rubuta rahoto a kai. Sai dai ban kai ga mika sakamakon ba sai Allah Ya sa AbduLsalam ya sauka daga shugabancin kasa ya mika mulki ga Obasanjo.

Daga baya mun mika rahoton ga sabon Shugaban Kasa Obasanjo tare da ci gaba da gudanar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta tallafa a kai, sai dai ba a kai ga samun nasarar aiwatar da rahoton tsare-tsaren ba a aikace.

Aminiya: Wadanne irin ayyuka kuka yi zuwa yanzu?

Dokta ’Yammama: Mun yi ayyuka da dama a kan haka daga ciki akwai wanda muka aiwatar a Karamar Hukumar Batagarawa da ke Jihar Katsina inda muka sayi wani makeken fili mai girman hekta kamar 370 muka tara jama’a daga unguwanni 6 na bayan garin. Abu na farko da muka yi shi ne gina musu makaranta mai aji 4 a maimakon tattaki da kananan yaransu ke yi daga yankin zuwa garin Batagarawa, sai rijiyar burtsatse da masallaci, sannan muka farfado da karamin asibitin da gwamnati ta yi musu wanda ya zamo kango inda muka zuba magunguna tare da kawo malaman jinya 2 daga Katsina don gudanar da wajen. Haka mun gina dakuna 5 a wajen don saukar da baki kamar malaman gona da gina babban dakin taro da cibiyar ba da dabarun noma, da aikin karamar hanya da ta hada wajen da kuma wata hanya da karamar hukuma ta yi. Akwai kuma matatar sarrafa itacen bi-ni-da-zugu da muka kafa don samar da wutar lantarki da kuma na’urar janareta 2 da ke amfani da man da muka sarrafa, daya janaretan na matatar ce dayan kuma shi ne ke bai wa cibiyar wuta da take bukata, sai kuma motar a-kori-kura ta cibiyar wadda ita ma ke amfani daga man da muke samarwa. Mun kuma ware kamar hekta 10 inda aka dasa itatuwan bi-ni-da-zugu a wajen bayan rainon itatuwan a wani waje daban da muka shuka. Su al’ummar ne ke yi mana dukan ayyukan kwadago da muke bukata sannan mu biya su in ban da aiki na kwarewa da muke dauko wadansu daga wani waje. Bayan mun fara sarrafa abin su da kansu sun ga amfanin man. Bayan nan mun dauki mutum 103 aiki daga cikinsu tare da koya musu yadda ake yin sabulun wanki da na wanke-wanke da ya hada da mota da na man kai da magungunan feshi da kendur duk daga sinadarin bi-ni-da-zugun. Wadannan ayyuka ne da ake yin su ba sai an yi makaranta ba kuma mun dauki ’ya’yansu da matansu muka ba su mabambantan ayyuka da za su dace da kowannensu.

Aminiya: Wace illa kake jin sare itatuwa ba tare da maye gurabensu ba za ta haifar?

Dokta ’Yammama: Ai ga shi nan muna gani. Ruwan sama da muke samu gwargwadon bukatar da yanayinmu ya kamata a ce ya samar babu shi, sakamakon sare itatuwan nan da kuma bacewar tsirrai. Sai dai ko a samu karancinsa ko kuma ya yi yawa a lokaci guda, inda hakan ke jawo ambaliyar ruwa da ke haifar da gushewar gidaje da kuma gonaki. Ambaliyar ruwan nan kashi biyu ne, akwai na cikin gari da toshewar magudanun ruwa da robobi ko kuma gina gidaje a kansu ke haifarwa. Sai kuma na wajen gari wadda gusowar hamada ke samarwa saboda rafuka su ma sun cike da kasa kasancewar saiwoyin itatuwa da suke rike kasa da magance zaizayarta babu su an sare su sai kasa ta yi ta kwaranyewa zuwa inda kwari ko rafi yake ta cike shi. Ga iskar guguwa tana kadawa ba tare da garkuwar da itatuwan nan ke samarwa ba. Dole ne gwamnati ta tashi tsaye ta samar wa jama’a da wani makamashi mai sauki da zai maye gurbin yin amfani da itatuwan nan ko gawayi, kamar makamashin iskar gas da kananzir ko kuma wanda ake sarrafawa daga ma’adanin kwal da sauransu. Ba wai kawai a kare a kan yin yekuwar hana sare itatuwa ba ko kona gawayi tare da an samar da abin da zai maye gurbinsa ba. Daga cikin gudunmawar da kungiyarmu ta bayar a wannan bangare akwai wani murhu da muka samar wanda ke amfani da sinadarin kwal da aka cire hayakinsa ta hanyar amfani da naurorin zamani sannan aka cura shi kamar girman gawayi. Mun hako shi ne da kuma gudanar da ayyuka a kansa tun daga cibiyar hakar ma’adinai na kwal ta Okaba Mining da ke Jihar Kogi. Shi kuma murhun an kera mana shi ne a wata cibiyar koyar da sana’a ta Talib da ke Malali, Kaduna bayan na nuna musu irin samfurin da muke bukata suka yi mana kamar guda dubu 1 kan sharadin kashi 70  cikin 100 na masu aikin zan dauko su ne daga makerar fanteka da ke Kaduna don su koyi yadda ake aikin da nufin ci gaba da yi don al’ummar kasa baki daya. Daga baya mun fadada aikin muka dauko karin wadansu yara daga wasu jihohin Arewa 12 mafiya fama da wannan matsala ta gusowar hamada, su ma suka koyi aikin. Ayyukan wannan kungiya sun kai ni wurare daban- daban ciki har da wani taron duniya da ya gudana a kasar Afirka ta Kudu a kan matsalar yaki da sauyin yanayi inda na samu ganawa da shugaban hukumar yaki da gusowar hamada da sauran matsaloli na muhalli a Majalisar Dinkin Duniya, wato  UNEP a takaice.

Aminiya: A karshe wane karin shawara za ka bai wa gwamnati da jama’a?

Dokta ’Yammama: A gaskiya matukar gwamnati ba ta tashii tsaye ta dakushe wannan matsala, ta hanyar fadakar da jama’a da kuma samar masu da wata mafita maimakon sare itatuwan da a ke yi ba tare da maye gurabansu ba. To wannan matsala ta ambaliyar ruwa za ta ci gaba da muni a kullum lokacin damina. Sannan idan rani ya zo a rasa ruwan gudanar da noman rani da na amfanin jama’a saboda ruwan zai ci gaba da tsotsewa ko kafewa daga inda aka saba samunsa a cikin sauki kasancewar yana shigewa cikin kasa cikin sauri maimakon adana shi a kurkusa da waje mai yanayin laka ke yi wanda kasa mai yanayin yashi ba za ta yi ba.